Mafi akasarin makaratun 'Yan Mata na jihar Kano ba su da damar amfani da Yanar Gizo - Bincike

Mafi akasarin makaratun 'Yan Mata na jihar Kano ba su da damar amfani da Yanar Gizo - Bincike

A wani bincike da cibiyar fasahar zamani da kawo ci gaba ta CITAD (Centre for Information Technology and Development) ta gudanar ya bayyana yadda kaso 95 cikin 100 na makaratun 'yan mata a jihar Kano ba su samun damar amfani da yanar gizo.

Shugaban wannan cibiya Mallam Yunusa Zakari Ya'u, shine ya bayyana hakan a yayin da ya jagoranci tawagar mambobin cibiyarsa wajen ziyarar shugaban reshen hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ta jihar Kano, Mallam Adamu Amshi.

A ziyarar ta kwana-kwanan nan, Ya'u ya bayyana cewa har ta a cikin makarantun dake samun dama ta kaiwa ga yanar gizo su na fama da wasu matsalolin dake kawo tagarda a cikin lamarin dake dakile amfanin ga dalibai.

Mafi akasarin makaratun 'Yan Mata na jihar Kano ba su da damar amfani da Yanar Gizo - Bincike
Mafi akasarin makaratun 'Yan Mata na jihar Kano ba su da damar amfani da Yanar Gizo - Bincike

Cibiyar ta gudanar da wannan bincike cikin makarantu 214 na 'yan Mata dake jihar Kano yayin da kaso 5 ne cikin 100 ke samun dama ta kaiwa ga yanar gizo, inda a wanan hali bincike ya nuna su kan su su na fama da matsaloli ko na rashin na'ura mai kwakwalwa ko kuma rashin malamai da suka yi nazari a fannin fasahar watsa bayanai ta zamani.

KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje ya bayyana dalilin Takun Saka tsakanin sa da Sanata Kwankwaso

Legit.ng ta fahimci cewa, a wani sa'ilin kuma akan samu tangarda ta rashin wadatacciyar wutar lantarki da za ta kawo tsaiko wajen amfani da yanar gizo.

Shugaban cibiyar ta CITAD ya kuma kirayi gwamnatin jihar akan samar da dama ga makarantun mata ta kaiwa ga fasahar yanar gizo wanda a wannan zamani ya zamto tamkar daya dayan 'yancin 'yan Adam.

Ya kuma buga misali dangane da rashin sa'ar dalibai da dama a jarrabawar JAMB ta kwana-kwanan nan a sakamakon karancin ilimin na'ura mai kwakwalwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng