Tsakanin Daurawa, diyar gwamna Ganduje da 'yan hakika: Sharhin marubuci

Tsakanin Daurawa, diyar gwamna Ganduje da 'yan hakika: Sharhin marubuci

Wannan Sharhi na marubuci Mubarak Bala ne, daga Kano, 08032880989, ba lallai ra'ayin gidan jaridar naji.com ba

- Sheikh Aminu Daurawa yace sun kama mai sabo ga addinin Islama a Kano, suna kuma neman hukuncin kisa ga alama

- Daurawa shine shugaba hukumar Hisba a Kano, mai tabbatar da shari'ar da ko Saudiyya ta fara saki

- A baya yace ya bar masu badala a Kano da Allah, saboda masu badalar yaran manya ne

Tsakanin Daurawa, diyar gwamna Ganduje da 'yan hakika: Sharhin marubuci
Tsakanin Daurawa, diyar gwamna Ganduje da 'yan hakika: Sharhin marubuci

A wannan zamani na ilimi da 'yancin fahimta, jihar Kano ta zabi ta zauna karkashin mulkin mulukiyyar larabawa daga yankin gabas ta tsakiya, inda duk abin da zatayi, sai ya daidaita da yadda al'adun yankin, ko addininsu ya fadi.

Hukumar Hisba ta Kano, wadda ta kasa kama kowa a lokacin bikin farin ciki da aka yi na diyar Gwamna Ganduje, duk da cewa, ma'aikatan hisbar suna cikin birnin, ta fito tace wadansu abubuwan baza ta iya kama wa ba, inda shugaban hukumar yace ya barsu da Allah.

Sai gashi a wannan makon, Shehun malamin, Aminu Ibrahim Daurawa, yana bada bayanai kan kama wani almajiri wanda yayi waqar yabon Shaihunsa, wai kuma ya kuma kushe wani abin bautar daban, kamar dai yadda shima addinin Islama yake kushe wasu ababen bautar da cimmasu.

DUBA WANNAN: Rigimar Larai da Turai: Janar daga Iran ya mayar wa da Saudiyya martani

Kama wannan yaron dai, dan Shekara 16-22, wanda almajiri ne daga kudancin Kano, ya nuna Shariar Islama a jihar Kano, ta talakawa ce da masu karamin karfi, shi kuwa mai kudi, sai yayi bushasharsa amma wai ai 'a barshi da Allah'.

A fahimta ta, kowa yana da 'yancin albarkacin bakinsa, yana kuma da 'yancin yayi ko yaki yin addini. Cin zarafin wani mai rai, ko zaginsa da cin mutuncinsa, ba daidai bane. Amma cin mutuncin ababen bauta, ko addinai, wannan bashi da wani ma'auni na cewa an cuci wani.

Addini ko ra'ayi, ba mutum bane, Allah ba mutum bane, babu wanda yaga addini na kuka ko abin bauta na cewa ya cutu daga wani cin zarafi da wani yayi masa, don haka ba laifi bane in an kushe su ababen bautar, walau Allah ko Shaidan, walau Aljan ko tsumburbura, ko da kuwa wasu suna bauta musu.

Shima kansa addinin Islama, ya ginu ne bisa cima wasu addinai da kuntata musu, ya zagi kafirai, ya kuma tsine da kushe gumaka, ya kyamace su, wanda shima in haka ne, da sai ace an ci zarafin gumakan ko an cuci masu bauta musu.

Don haka, kamata yayi a saki wannan yaron, a kyale 'yan fim, da 'yan hakika suyi irin tasu rayuwar, ko nasu addinin, in akwai Allah zai bi hakkinsa da kansa, in kuma babu, shikenan, barhama ya huta.

Ya kamata musulmin Najeriya su waye, su san darajar dan-Adam tafi darajar ababen bauta. Ko Saudiyya ta fara farga.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel