Gwamna Ganduje ya bayyana dalilin Takun Saka tsakanin sa da Sanata Kwankwaso

Gwamna Ganduje ya bayyana dalilin Takun Saka tsakanin sa da Sanata Kwankwaso

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana babban dalilin da ya sanya suka shiga takun saka tsakanin sa da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Kamfanin watsa labarai na Channels TV ya ruwaito yadda cewa gwamna Ganduje ya yi wannan karin haske dangane da sabanin tsakanin sa da tsohon ubangidan sa a yayin ganawa cikin wani shiri mai taken Roadmap 2019 da kamfanin ya watsa a ranar Litinin 23 ga Afrilu.

Legit.ng ta fahimci cewa, tabbasa gwamnan cikin ganawar sa da manema labarai ya amince da rashin 'yan ga maciji dake tsakanin sa da Kwankwaso, inda yake cewa sun sabani ne a sanadiyar bambancin salo na gudanar da shugabanci.

Gwamna Ganduje ya bayyana dalilin Takun Saka tsakanin sa da Sanata Kwankwaso
Gwamna Ganduje ya bayyana dalilin Takun Saka tsakanin sa da Sanata Kwankwaso

Ganduje yake cewa, "duk mutumin da ya kasance a kujerar gwamnatin ya kan so mai gajiyar wannan kujera ya ci gaba da gudanar da tsarin gwamnatin a salo makamancin na sa, sai dai ko shakka babu har ta 'yan tagwaye su kan bambanta ta fuskar halayya."

Gwamnan ya kuma yi fashin baki dangane a cewa ba bu yadda za a yi su gujewa afkuwar wannan sa'insa tsakanin sa da tsohon Ubangidan sa domin kuwa wani ba sabo abu bane cikin tsari na dimokuradiyya.

Sai dai gwamnan ya tabbatar da cewa, sa'insa tsakanin su za ta kawo karshe kasancewa su na gudanar da ita ne cikin wayewar kai da kuma fahimta.

KARANTA KUMA: IG na Kasa ya nemi a binciki yadda Sanata Dino Melaye ya kubuce daga hannun Jami'an Tsaro

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Ganduje ya kasance mataimakin gwamna a lokacin gwamnatin Kwankwaso a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003 da kuma karo na biyu a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015, inda ya ci gajiyar kujerar gwamnan a shekarar 2015.

A yayin haka kuma, gwamna Ganduje ya bayyana kudirin sake neman takarar kujerar sa sakamakon huro wuta na magoyan bayan sa kan aikata hakan dangane da nasarorin da gwamnatin sa ta samu kamar yadda bayar dalili.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel