Hukumar INEC zata bi diddigin kudin da jam'iyyu zasu kashe yayin yakin neman zabe

Hukumar INEC zata bi diddigin kudin da jam'iyyu zasu kashe yayin yakin neman zabe

- Hukumar INEC zata sa ido a kan kudaden da jam'iyyu zasu kashe a kamfen na zaben 2019

- Kwamishinan sa ido kan zabe na INEC, Alhaji Baba Shettima Arfo ne ya fadi haka a wani taro da aka gudanar a ranar Laraba

- Za'a horas da mahalarta taron dabarun yadda ake binciko kudaden da yan takara da jam'iyyu ke kashe da yadda ake rubuta rahoto

Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa wato (INEC) tace zata sanya ido akan kudin da jam'iyoyi da yan takara ke rzasu kashe a kan harkar yakin neman zabe na shekara ta 2019.

Kwamishinan kula da harkokin zabe da jam'iyu na hukumar, Alhaji Baba Shettima Arfo ne ya bayyana hakan a wani taron karawa juna sani da ake gudanarwa na kwanaki kwana biyu a Gombe inda za'a horas ta ma'aikatan dabarun bin didigin kudaden da yan siyasar ke kashewa.

Hukumar INEC zata bi diddigin kudin da jam'iyyu zasu kashe yayin yakin neman zabe
Hukumar INEC zata bi diddigin kudin da jam'iyyu zasu kashe yayin yakin neman zabe

DUBA WANNAN: Tsaka mai wuya: An fara tantance saka hannun masu son yiwa Dino Melaye kiranye

Da yake jawabi a madadin kwamishina hukumar zaben, Alhaji Umar Ibrahim, yace an shirya taron karawa juna sanin ne domin koyar da dabarun yadda ake kula da yanda ake amfani da kudi wajen yakin neman zabe da aikewa da rahoto.

Yace mahalarta taron da aka gayyata daga jihohi 6 dake yankin tare da ma'aikatan CBN, EFCC da kuma NBC zasu koya yadda ake bincike kan kudaden da yan takara ke kashewa tare da kudaden da jami'iyyu ke kashewa da yadda ake rubuta rahoto.

Yace taron yana cikin jerin aikin da hukumar zata gudanar domin gano adadin lkudaden da jam'iyyun siyasa da yan takara ke kashewa yayin yakin neman zaben wanda yace hakan nada matukar muhimmanci ga cigaban demokradiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel