Ashha! An kara kashe wasu mutane 34 a sabon hari a jihar Benuwe

Ashha! An kara kashe wasu mutane 34 a sabon hari a jihar Benuwe

A kalla mutane 34 ne suka mutu a wasu garuruwa biyu dake karamar hukumar Guma na jihar Binuwai. Wanna ya afku ne bayan kisan kiyashi da akayi wa limaman coci biyu tare da mabiyansu 17 a garin Gwer na jihar ta Binuwai.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kai harin ne a garin tse Agudu da ke Mbawar da kuma Tse Mbadwem dake Mbakpaase duk a karamar hukumar Guma daga daren ranar Talata zuwa safiyar jiya Laraba.

Yanzu-Yanzu: An kashe mutane 34 a wata sabuwar hari da aka kai kauyukan jihar Benuwe
Yanzu-Yanzu: An kashe mutane 34 a wata sabuwar hari da aka kai kauyukan jihar Benuwe

Wani mazaunin garin, Cletus Keve, ya shaidawa manema labarai cewa yan bindigan sun iso garin ne sanye da kayan sojoji kuma suka fara kai hari a Tse Ali Agudu misalin karfe 4 na asuba a jiya inda suka kashe mutane da dama.

KU KARANTA: Wata sabuwar rikici ta barke a Nasarawa, mutane 15 sun riga mu gidan gaskiya

Keve ya cigaba da cewa, a halin yanzu an gano gawawaki 19 sannan wasu mutanen da suka sami raunuka suna asibiti inda ake basu kulawa da magunguna.

Hakazalika, wani mai takarar gwamna a jihar, Dr. Tovlumun Nyitse, wanda dan asalin karamar hukumar Guma ne, ya fadawa manema labarai a garin Makurdi cewa an gano gawawaki 15 a cikin daji a garin Mbadwen duk dai a karamar hukumar na Guma.

Nyitse yace a wasu garuruwan, ba'a kashe mutane ba sai dai an kona gidaje, kayayakin abinci da wasu dukiyoyin mutane a harin da aka kai musu misalin karfe 11.30 na daren Talata.

Mazauna kauye sun ce yawancin wadanda aka kashe mutanen da suka dawo daga sasanin yan gudun hijira ne.

Kwamishinan Yan sanda, Fatai Owoseni, yace bashi da cikaken bayanin akan abinda ya faru saboda haka ba zai iya yin tsokaci ba akan lamarin a lokacin da ake rubuta wannan rahoton.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel