Wata sabuwar rikici ta barke a Nasarawa, mutane 15 sun riga mu gidan gaskiya
- Rikicin sarauta tsakanin kabilai biyu a Nasarwa yayi sanadiyar mutuwar mutane da kone-konen dukiya
- Rikcin ya faru ne a garin Umaisha dake karamar hukumar Toto na jihar Nasarawa
- Yan sanda sun tabbatar da afkuwar harin kuma sunyi nasarar kama mutane biyu da ake zargin suna cikin maharan
A kalla mutane 15 ne suka rasa rayyukansu sakamakon barkewar wata rikici a tsakanin mutanen kabilar Bassa da Egbura wanda suka zaune a garin Umaisha dake karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa.
Daily trust ta ruwaito cewa kabilun biyun sun dade suna jayaya da juna saboda saurauta wanda dukkan garuruwan biyu suna son sarautar ta zauna a garin nasu.
KU KARANTA: 'Yan kasuwa 80 masu tauye mudu sun shiga hannun hukumar Hisbah
Wani ganau, Abdullahi Haruna, ya shaidawa manema labarai cewa yan kabilar Bassa sun bijiro wa mutanen garin Umaisha a daren jiya Litinin inda suka fada cikin garin suna ta karbe mutane har misalin karfe 5 na asuba.
Duk da cewa Abdullahi yace mutane biyu ne suka rasu a jiya, wani majiyar ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa adadin mutanen da suka mutu ya kai 15.
Mai magana da yawun yan sandan Jihar Nasarawa, DSP Idrisu Kennedy, ya tabbatar da afkuwar harin amma bai tabbatar da adadin wanda suka mutu ba. "Bamu samu rahoton adadin mutanen da suka mutu ba amma dai mun san cewa an kona gidaje da motoci yayin kai harin," inji Kennedy.
Kennedy ya cigaba da cewa, hukumar Yan sandan ta kama mutane biyu da ake zargin suna cikin gungun mutanen da suka kai hari a garin in Umaisha, ya kuma kara da cewa, "Yan sanda sun fatataki maharan kuma sun kama guda biyu, an sami bindigogi 7 tare da su."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng