'Yan kasuwa 80 masu tauye mudu sun shiga hannun hukumar Hisbah

'Yan kasuwa 80 masu tauye mudu sun shiga hannun hukumar Hisbah

- Hukumar Hisbah na Jihar Sakkwato tayi dirar mikiya a kan masu yauye ma'auni

- Hukumar ta kama yan kasuwa 80 yayin da ta kai samame a babban kasuwar Sakkwato

- Hukumar tace tauye ma'auni haramun ne kuma a baya an gargadi yan kasuwan a kan hukuncin yin hakan

Hukumar Hisbah na Jihar Sakkwato ta bayar da sanarwan kama 'yan kasuwa masu sayar da hatsi guda 80 a babban kasuwa Sakkwato bayan an same su da laifin tauye ma'aunin da suke amfani dashi wajen yin awo.

'Yan kasuwa 80 masu tauye mudu sun shiga hannun hukumar Hisbah
'Yan kasuwa 80 masu tauye mudu sun shiga hannun hukumar Hisbah

Hukumar tace, abinda da yan kasuwar suka aikata ya janyo suna tauhe hakkin mutane da ke zuwa siyaya a wurinsu domin canja yanayin ma'aunin yana rage adadin hatsin da ake auna wa musamman shinkafa da gero.

KU KARANTA: Hotunan rantsar da gwamna Badaru a aikin da jam'iyyar APC ta bashi jagoranci

Kwamandan hukumar na Jihar, Dr. Adamu Bello Kasarawa, yace ya kamata a samu mudu 40 ne cikin buhun hatsi amma hakan na raguwa zuwa 30 da yan kai, saboda haka ya zama dole a takawa masu irin wannan halaya birki.

Kasarawa ya kara da cewa tauye ma'auni ya sabawa dokokin addinin musulunci, kuma hukumar ta gudanar da fadakarwa na musamman a baya inda ta gargadi yan kasuwan a kan haramcin tauye mudun da kuma hukuncin da ka iya biyo baya.

Shugaban yace hukumar ta kai ziyara wasu kananan hukumomi ne don tabbatar da cewa yan kasuwan basu ha'intar masu zuwa siyaya a wajensu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: