Yadda Kwayoyin halittu ke habaka da sanadin Barasa wajen dakile wasu cututtuka a jikin dan Adam

Yadda Kwayoyin halittu ke habaka da sanadin Barasa wajen dakile wasu cututtuka a jikin dan Adam

A wani sabon bincike da aka gudanar ya tabbatar da yadda wasu kwayoyin halittu na Bacteria ke habaka wajen dakile haddasanar cututtukan dasashi, ciwon daji watau Kansa da kuma nau'ikan cututtuka da suka shafi zuciya ga masu ta'ammali da barasa.

An wallafa wannan sabon bincike ne a mujallar Microbione inda ta bayyana karara cewa, akwai wasu nau'ikan kwayoyin halittu na bacteria dake habaka a bakunan masu ta'ammali da barasa wadanda kuma suke dakile habakar wasu kwayoyin cututtuka masu lahani ga lafiyar dan Adam.

Legit.ng ta fahimci, an gudanar da wannan bincike ne a jami'ar nazarin Lafiya dake birnin New York na kasar Amurka da sanadin wata kwararriyar likita akan nazarin cututtukan mutane, Jiyoung Ahn.

Yadda Kwayoyin halittu ke habaka da sanadin Barasa wajen dakile wasu cuttuka a jikin dan Adam
Yadda Kwayoyin halittu ke habaka da sanadin Barasa wajen dakile wasu cuttuka a jikin dan Adam

Jiyoung Ahn dai ta bayyana cewa, duk da kasancewar cututtukan zuciya, dasashi da kuma na Daji su kan kama masu ta'ammali da barasa da karan sigari, akwai kuma kwayoyin halittu da barasa ke habakarwa a baka da suke taimakawa wajen dakile cututtukan su kansu.

KARANTA KUMA: Hotunan wurare 5 da ya kamata ku ziyarta a garin Abuja domin bude idanu

Binciken ya tabbatar da cewa, akwai kimanin adadin kwayoyin halittu 700 na bacteria a Baka, wadanda ke kawo zagon kasa ga cututtukan da suke afkuwa a sakamakon ta'ammali da barasa.

Ire-iren wannan kwayoyin halittu masu dakile cututtukan su kan habaka a yayin da aka yi ta'ammali da barasa. Kadan daga cikin kwayoyin halittun sun hadar da; Bacteroidales, Actinomyces, Neisseria da kuma Lactobacillales da ake samu cikin wasu nau'ikan abinci kuma suke taimakawa wajen hana kamuwa da rashin lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng