Da yaki biyawa jama'a zuwa aikin hajji tun bayan hawansa gwamna, dubi nawa ya tseras wa lalitar jiharsa

Da yaki biyawa jama'a zuwa aikin hajji tun bayan hawansa gwamna, dubi nawa ya tseras wa lalitar jiharsa

Kwamishinan aiyukan cikin gida na jihar Legas, Dr Abdulhakeem Abdullateef ya bayyana yanda kin daukar nauyin mahajja zuwa makka da Jerusalem da Gwamna Akinwunmi Ambode yayi ya adana Naira biliyan 4.5 na jihar a cikin shekaru uku.

Da yaki biyawa jama'a zuwa aikin hajji tun bayan hawansa gwamna, dubi nawa ya tseras wa lalitar jiharsa
Da yaki biyawa jama'a zuwa aikin hajji tun bayan hawansa gwamna, dubi nawa ya tseras wa lalitar jiharsa

Dr. Abdullateef ya bayyana hakan ne a ganawa da manema labarai don tsokaci akan cigaban da aka samu na mulkin shekaru uku karkashin shugabancin Gwamna Ambode.

Kamar yanda yace waccan Gwamnatin da ta wuce tana amfani da Naira biliyan 1.5 don daukar nauyin mahajjata a duk shekara.

"A lokacin da Gwamna Ambode ya hau mulkin, ya jaddada cewa babu zancen daukar nauyin kowa zuwa saudia ko Isra'ila. Yace Gwamnatin dai zatayi kokarin samar duk abinda ya dace na walwala ga mahajjatan ko a wajen kasar."

"Ta wannan matakin ne mukayi nasarar adana Naira biliyan 4.5 wanda zamuyi amfani dasu don gyaran tituna da kuma aiyukan cigaba a jihar."

DUBA WANNAN: Yawan yaran da aka ceto daga almajirta a jihar Kano ya zuwa yanzu

Abdullateef ya ja kunnen bangarorin addini da su guje rufewa mutane tituna don Gwamnatin jihar bazata amince da hakan ba.

"Akwai wuraren da sallah bata karbuwa. In kuka rufe tituna kuna sallah bazata karbu ba. Nima babban limami ne kuma nasan abinda nake cewa. Tituna ba gurin bauta bane. In jam'in yayi yawa toh ku raba lokutan sallah."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng