Bayan da matarsa ta rasu a makon jiya, shugaba Bush na Amurka na can rai ga hannun Yesu
- Shugaban ya aure ta shekaru 73 da suka wuce kuma ta mutu tana 92
- Shima dama shekarunsa sun kai 90 da doriya
- Sun sha fada cewa zasu hade a aljanna, ko bara yayi rashin lafiya
A birnin Texas an ruwaito cewa shugaba Bush na Amurka, wanda ya mulki kasar ta Amurka a 1988-1992 yana can rai ga hannun Allah a wani asibiti na kwararru, inda ake kokarin ceto ransa. Mai shekaru 96, Bush, ya sami cutar da ta ratsa jininsa a jiya.
A makon jiya ne dai ya rasa uwargidansa wadda ta rasu bayan da ta kai shekaru 92 da haihuwa. Ta aure shi tun duniya ba kala, kuma sun yi zaman aure shekaru 73.
Sun haifi 'ya'ya da suka tsunduma a siyasa, inda shima dansu ya mulki Amurka a 2001-2009. Wanda ya nuna ta auri shugaban kasa ta haifi shugaban kasa.
DUBA WANNAN: Yawan yaran da aka ceto daga almajirta a jihar Kano ya zuwa yanzu
Shi shugaba Bush wanda yake asibitin shine yayi yakin Saddam Hussaini na farko, wanda ake kira Gulf War, inda ya kwato Kuwaiti daga hannun Saddam Hussain, wanda ya mamaye ta don shan mai da danniya.
Dansa kuwa, Bush na biyu, shi ya tumbuke Saddam har ya kai ga aka rataye shi kan kashe 'yan shia a Iraki a Halabja da Basra.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng