Taron Jama’a sun fito tarbar Tsohon Gwamnan Kano a Jihar Sokoto

Taron Jama’a sun fito tarbar Tsohon Gwamnan Kano a Jihar Sokoto

- Mutane sun fito kan hanya lokacin da su ka ji labarin Kwankwaso ya je Sokoto

- Sanatan kasar ya kai ziyara Jihar Sokoto ne domin halartar wani daurin aure

- Babban ‘Dan Majalisar dai yana samun dinbin magoya baya duk inda ya shiga

Jama’a da dama sun fito kan titi lokacin da tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai ziyara Jihar Sokoto domin halartar wani daurin aure a karshen makon da ya wuce.

Taron Jama’a sun fito tarbar Tsohon Gwamnan Kano a Jihar Sokoto
Tsohon Gwamnan Kano tare da Oyegun a Jihar Sokoto

Tsohon Gwamnan na Kano ya halarci bikin ‘daurin auren Dr. Saratu Abubakar Gobir da kuma Habibu Mohammed Abubakar kamar yadda ya bayyana da kan sa a shafukan sada zumunta na Tuwita a karshen makon na jiya.

KU KARANTA: An shigar da Sanatocin Najeriya kara a Kotu

Taron Jama’a sun fito tarbar Tsohon Gwamnan Kano a Jihar Sokoto
Dinbin Jama'a sun yi lale da zuwan Kwankwaso Garin Sokoto

A wajen bikin tsohon Gwamnan ya hadu da Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa John Oyegun. Kwanakin baya dai Sanatan ya je ziyara yankin domin yi wa jama’an Zamfara jaje.

Bayan nan Sanatan na Kano ta tsakiya ya gana da tsohon Kyaftin din ‘Yan kwallon Najeriya Kanu Nwankwo. Tsohon Dan kwallon da yayi tashe a kasar Ingila ya ci jar hular sa a lokacin da ya gana da babban Sanatan Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: