Banji dadin harin shaidanu a kan masu ibada ba, Buhari ya nuna bacin ran sa da harin Benuwe

Banji dadin harin shaidanu a kan masu ibada ba, Buhari ya nuna bacin ran sa da harin Benuwe

- Shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyar sa ga gwamnati da mutanen jihar Benuwe sakamakon harin da wasu yan bindiga suka kai a jihar

- An kai harin ne a Cocin St. Ingantius na garin Ukpor-Mbalom inda aka kashe limamai biyu tare da wasu mabiya da yawa

- Shugaban kasan yace wannan aikin shedanu ne kuma ya dau alwashin binciko su don su fuskanci hukunci

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana harin da aka wani Coci inda aka kashe limaman cocin biyu da wasu mabiyansu a matsayin rashin rashin imani da wasu shedanun mutane suka aikata. An dai kai harin ne a yau Talata a Ukpor-Mbalom dake karamar hukumar Gwer ta gabas a jihar Benuwe.

Sakon nuna shugaba Buhari na kunshe ne cikin wata sanarwan na musamman da ta fito daga bakin mai bawa shugaban kasa shawara na musamman ta fanin kafafen yadda labarai, Femi Adesina.

Banji dadin harin shaidanu a kan masu ibada ba, Buhari ya nuna bacin ran sa da harin Benuwe
Banji dadin harin shaidanu a kan masu ibada ba, Buhari ya nuna bacin ran sa da harin Benuwe

KU KARANTA: Dalilan da suke kawo cikas a bangaren samar da wutar lantarki - Fashola

Buhari ya kara da cewa wannan harin da aka kai wa limaman da mabiyansu wani yunkuri ne na musamman da akyi don tayar da rikicin addini tsakanin mabiya addinan da suke zaune a wannan garuruwan wanda kawai zai haifar da zubar da jini ne.

Ya kuma ce gwamnatinsa ba zata sanya idanu ta bari wasu azzalumai su hargitsa kasar nan ba, hakan yasa yayi alkawarin gudanar ba bincike don gano wanda sukayi wannan aika-aikan don su fuskanci hukunci.

Shugaban kasar, ya kuma mika sakon ta'aziyarsa ga gwamnatin Jihar Benuwe da mutanen jihar musamman mazauna garin Mbalom, da kuma Bishof da limaman cocin da sauran masu bauta a Cocin St. Ignatius Catholic Church inda yan bindigar suka kai hari.

Yace shedanu ne kawai zasu iya zuwa wajen bauta su kashe limamai da sauran masu bauta kawai don su tayar da fitina da zata haifar da zubar da jinin mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164