Yanzu:yanzu: Dino Melaye ya kubuce daga hannun ‘yan sanda, wasu tsageru ne suka kwace shi

Yanzu:yanzu: Dino Melaye ya kubuce daga hannun ‘yan sanda, wasu tsageru ne suka kwace shi

- A jiya ne jami'an hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) ta hana Sanata Dino Melaye ficewa daga Najeriya bisa umar hukumar 'yan sanda

- Tun jiya aka girke jami'an 'yan sanda a kofar gidan Sanata Melaye bayan hana shi ficewa zuwa kasar Morocco tare da wasu Sanatoci

- A yau da safe kuma jami'an 'yan sanda suka kama sanatan duk da korafin da yake yi na cewar ana muzguna masa

An samu hatsaniya a shataletalen Area 1 dake Abuja inda wasu tsageru da ake zaton magaoya bayan Sanata Dino Melaye ne suka datse ayarin jami’an ‘yan sanda dake dauke da sanatan (mai wakilatar Kogi ta yamma) sannan suka kwace shi daga hannun jami’an duk da suna dauke da makamai.

An fara sa-in-sa tsakanin jami’an tsaro da tsagerun matasan da misalign karfe 2:10 na rana kuma ta dauki kimanin mintuna shida kafin matasan dake cikin motoci biyu kirar Toyota Hilux su dauke sanata Melaye su saka shi a motar su sannan suka zaburi motocin su suka bar wurin tare da tayar kura.

Yanzu:yanzu: Dino Melaye ya kubuce daga hannun ‘yan sanda, wasu tsageru ne suka kwace shi
Dino Melaye ya kubuce daga hannun ‘yan sanda, wasu tsageru ne suka kwace shi

Tun a jiya jami'an hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) bisa umarnin hukumar 'yan sanda ta dakatar da Sanata Melaye daga fita daga Najeriya zuwa kasar Moroko tare da wasu Sanatoci.

DUBA WANNAN: Fusatattun 'yan Achaba sun sun lakadawa wani VIO na jaki Abuja, karanta dalili

Hukumar 'yan sanda ta girke jami'an ta a gaban gaban gidan Sanatan tun jiyan, wani lamari dake nuni da cewar suna tunanin zai iya sulalewa daga gidan ya bar kasar.

Da safiyar yau ne jami'an hukumar 'yan sanda suka kama Sanata Melaye suka tafi dashi ofishin su domin amsa tambayoyi bisa zargin da hukumar ta dade tana yi masa na amfani da wasu 'yan ta'adda domin tayar da fitina a jihar Kogi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel