'Yan sandan Najeriya sun dakile wani mummunan harin kunar bakin wake a jihar Borno
Hukumar 'yan sanda a jihar Borno ta tabbatar da cewar jami'an ta sun dakile wani harin kunar bakin wake a karamar hukumar Bama.
Hukumar ta ce jami'an ta sun yi nasarar cafke uku daga cikin maharan kafin su kai ga inda zasu fasa bam din da suka dauro a daren jiya.
Yunkurin harin na zuwa ne cikin abin da bai wuce sa'o'i 24 ba da wasu 'yan harin kunar bakin wake biyu, mace da namiji, suka kashe a kalla mutane bakwai a wani masallaci a Bama yayin sallar Asuba.
Jama'ar garin Bama, mai nisan kilomita 70 daga Maiduguri, sun fara komawa garin su a wannan watan, Afrilu, bayan shafe shekaru hudu a sansanin 'yan gudun hijira.
DUBA WANNAN: Dalilin da yasa kasafin kudin shekarar bana ba zai samu wucewa ba yau
A jawabin da kakakin hukumar 'yan sanda a jihar, DSP Edet Okon, ya fitar a yau, Talata, ya ce "A jiya Litinin da misalin karfe 10:00 na dare wasu jami'an mu suka dakile wasu 'yan harin kunar bakin wake da suka yi kokarin shigowa Bama ta yankin Ajilari duk da maharan sun tashi bam din amma su kadai ne suka mutu."
Kwamishinan 'yan sandan jihar Borno, CP Damian Chukwu, ya ce yanzu haka al'amura sun dawo daidai a garin Bama tare da bukatar jama'a su koma bakin harkokin su ba tare da fargaba ko tsoro ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng