Wata kungiya ta maka wasu fulogai daga cikin sanatoci a kotu

Wata kungiya ta maka wasu fulogai daga cikin sanatoci a kotu

- Wata kungiya mai suna SERAP, da maka shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da wasu Sanatocin a kotu a kan allawus din N13.5m da suke karba duk wata

- A cikin kwanakin nan Sanata Shehu Sani na Jihar Kaduna ya fadi cewa kowanne Sanata karbar allawus din N13.5m duk wata

- Kungiyar tace wannan karabar wannan allawus zamba ce da cuta kuma hakan ya sabawa doka

Wata kungiyar mai zaman kanta mai suna 'Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP), ta bukaci babban kotun tarayya dake Legas ta umurci Sanata Bukola Saraki, Sanata Dino Melaye da sauran takwarorinsu 107 su mayar da allawus din N13.5m da suke karba duk wata kuma a dakatar da bayar da allawus din wanda kungiyar tace ya sabawa kundin tsarin kasa.

Wata kungiya ta maka wasu fulogai daga cikin sanatoci a kotu
Wata kungiya ta maka wasu fulogai daga cikin sanatoci a kotu

A rahoton da jaridar Vanguard ta ruwaito, SERAP, har ila yau tana rokon kotun ta bayar da umurnin bincike akan yadda kowane Sanata ya kashe kudaden allawus din aiki da ake bawa kowane Sanata don samar da ababen more rayuwa ga mutanen yankin da yake wakilta kuma a bayyana wa mutane sakamakon.

KU KARANTA: Hotunan rantsar da gwamna Badaru a aikin da jam'iyyar APC ta bashi jagoranci

Legit.ng ta gano cewa a takaradan karar da SERAP ta shigar mai lamba FHC/L/CS/630/18 a ranar Litinin 23 ga watan Afrilu, Kungiyar ta nuna kin amincewar ta da hujjar ta majalisar ta bayar na cewa wannan kudin yana cikin kudaden kula da lafiya ne da tafiye-tafiye, inda tace akwai wani sashin kudirin dokar daya fayyace kudaden kula da lafiya da tafiye-tafiyen.

SERAP ta gano wannan kudaden allawus din da Sanatacin ke karba ne bayan Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya bayyana cewa shi da takwarorinsa suna karabar N13.5m duk wata bayan sun karbi albashinsu da sauran allawus.

A wata rahoton Legit.ng ta kawo a baya, kun karanta cewa hukumar tattara haraji na Revenue Mobilisation Allocation and Foscal Commission (RMAFC) ta bayyana cewa Sanatoci na karbar N1.06m ne duk watan a amatsayin albashi da allawus duk wata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel