Hotunan rantsar da gwamna Badaru a aikin da jam'iyyar APC ta bashi jagoranci
An nada Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar domin ya jagoranci kwamitin shirye-shiryen babban taron jam'iyyar APC mai mambobi 68. An ƙaddamar da Kwamitin ne a Hedikwatar Jam'iyar APCn dake Abuja a jiya Litinin.
Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo shi zai zama mataimakin Shugaban Kwamitin a yayin da Sanata Ben Uwajumogu zai kasance magatakardan kwamitin.
DUBA WANNAN: Dalilan da suke kawo cikas a bangaren samar da wutar lantarki - Fashola
Gwamna Badaru ya yi alƙawarin aiki tuƙuru domin samun nasarar babban taron, a yayin da ya kuma yi alƙawarin zai yi aiki da duk mambobin kwamitin.
Duk da cewa jam'iyyar bata tsayar da ranar da za'a gudanar da taron ba, sakataren tsare-tsare na kasa, Sanata Osita Izunaso, ya lisafa sauran mambobin kwamitin da suka hada da Sanata Ken Nnamani, Gwamna Rochas Okorocha, Kashim Shettima, Gwamna Aminu Bello Masari da Gwamna Abiola Ajimobi.
Sauran sun hada da Gwamna Ibrahim Gaidam, Gwaman Nasir El-Rufai, Gwamna Simon Bako Lalong, Gwamna Bindow M.U. Jibrilla, Gwamna Yahaya Bello da Gwamna Godwin Obaseki, Sanata Ahmed Sani Yarima, Adamu Aliero, Danjuma Goje, Abdullahi Adamu, George Akume, Chris Ngige da Ibrahim Abdullahi Gobir da wasu saura.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng