Atiku Abubakar yayi karin haske game da hana shi shiga kasar Amurka
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasar nan Alhaji Atiku Abubakar yayi karin haske game da maganar hana shi shiga kasar Amurka da ake ta yawo da ita.
Fitaccen dan siyasar da yanzu haka ke zaman babban jigo a jam'iyyar adawa ta PDP ya yi wannan harin haske ne lokacin da ya ziyarci sashen Hausa na BBC dake can birnin Landan.
KU KARANTA: Dalilin da ya sa na dawo rakiyar Buhari - Atiku
Legit.ng ta samu cewa da aka tambaye shi ko meye dalilin da ya sa shi baya zuwa kasar Amurka sai ya bayyana cewa tabbas ya ce ya nemi bizar shiga kasar, "amma sun hana ni." Kamar dai yadda ya ce.
Sai dai da aka tambaye shi dalilin hana shi bizar ta shiga Amurka ya ce shi ma ba a gaya masa dalili ba.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a watan Disamabar bara ne Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyya mai mulki ta APC, inda daga bisani ya koma jam'iyyar hamayya ta PDP.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng