A yau zan mika kaina ga jami'an 'Yan sanda - Dino Melaye

A yau zan mika kaina ga jami'an 'Yan sanda - Dino Melaye

- Sanata Dino Mealye yace zai tafi ofishin Yan sanda a yau don ya kare kansa da kuma talakawan Najeriya

- Wannan ya biyo bayan yunkurin kama Sanatan a jiya ne yayin da yake kokarin shiga jirgi zuwa kasar Morocco

- Melaye yace akwai masu nufinsa da sharri a kasar nan saboda yana fadin gaskiya kuma yana kokarin kare hakkin talakawa

Sanata Dino Melaye, mai wakiltan yankin Kogi ta yamma yace zai mika kansa zuwa ga hannun yan sanda a yau. Sanatan da aka dade ana rikici dashi ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter.

Kalamansa "A yau zanje wajen yan sanda domin na fadi gaskiya da kuma kare talakawan Najeriya. Za muyi nasara."

A jiya ne hukumar yan sanda ta kai masa mamaya a gidansa na Abuja.

A yau zan mika kaina ga jami'an 'Yan sanda - Dino Melaye
A yau zan mika kaina ga jami'an 'Yan sanda - Dino Melaye

Melaye wanda aka kama shi a filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikwe International Airport da misalin 7:30 na safe, ya tsere daga hannun hukumar a jiya bayan awa daya da kama shi.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kashe wani gawurtacen 'dan ta'ada a jihar Akwa Ibom

Daily trust ta bayyana cewa a lokacin da aka kama Melaye yana kan hanyarsa ta zuwa Morocco tare da deputy senate na shugaban kasa Ike Ekweramadu.

Melaye yace a lolacin da suka kirashi sunce masa ne suna da wata tattaunawa dashi da yaje kuma sai sukace masa an kamashi bisa umarnin yan sanda. Bayan wasu awanni Melaye ya koma gidan sa me lamba 11 sangha street maitama Abuja.

Melaye ya tsere ne daga wajen immigration a yayin da suke jiran isowar yan sanda.

Yan sanda sunyi kwantan bauna ne a cikin layin gidansa har zuwa karfe 7:00 na yamma. Wayar Melaye bata shiga kwatakwata amma sun tabbatar da cewa yana cikin gidansa.

Hukumar yan sanda tana zargin Melaye da safarar bindogogi da ake rabawa yan dabar jihar Kogi.

Da misalin 9:30 na dare ya bayyana a shafinsa na twitter cewa "an dauke duk wasu masu bashi tsaro wata PC ce tazo ta dauke su wanda hakan na daga cikin shirinsu na kamani, to da Allah na dogara kuma gaskiya zata bayyana." inji shi

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel