Babu doka da bin oda a Najeriya Inji Dino Melaya bayan an tsare sa

Babu doka da bin oda a Najeriya Inji Dino Melaya bayan an tsare sa

- Dino Melaya ya koka da halin da aka ciki na rashin doka a Najeriya

- Sanatan kasar yace ana neman ganin bayan sa kuma ya san da hakan

- Babban ‘Dan Majalisar yace babu fa wanda ya isa ya hana sa magana

Mun samu labari cewa ‘Dan Majalisar Dattawan kasar nan Sanata Dino Melaye wanda yayi fice ya fito jiya Litinin ya fadawa Duniya cewa fa ana nema a ga bayan sa. Hukumar NIS tace an ba ta doka daga sama cewa ta tsare Sanatan.

Babu doka da bin oda a Najeriya Inji Dino Melaya bayan an tsare sa
Hukumar NIS na Najeriya ta yi ram da Dino Melaya jiya

Sanata Dino Melaye wanda ya fada hannun Jami’an da ke lura da shige-da-fice a kasar jiya da safe lokacin da yake shirin barin Najeriya yayi bayani a kafofin sadarwa cewa an shirya yadda za a kashe shi kuma ya san da wannan shiri.

‘Dan Majalisar ya kara jadadda cewa shi mutum ne mai son bi doka kuma bai sabawa wata dokar kasa ba amma aka cafke sa. Sanatan yace babu takarda daga Hukuma kuma duk da maganar sa na Kotu amma aka kama shi aka tsare babu dalili.

KU KARANTA: Gwamnan Kaduna ya maka wani Talakan sa a Kotu

Sanatan yake cewa babu wanda ya isa ya hana masa magana domin kuwa ana zama ne cikin doka da tsarin mulki. Sanatan ya fadawa BBC cewa Hukumomin kasar sun wuce gona da iri domin kurum a ga bayan shi saboda maganganun da yake yi.

Dama can a baya Rundunar ‘Yan Sanda sun ce su na neman Sanatan wanda ya tubure yace bai aikata komai ba illa wasu ne ke neman ganin bayan sa. Sanatan dai ya saba cewa yana magana ne da yawun Talaka don haka ba ya tsoron Gwamnati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng