Atiku ma ya taba cewa ‘yan arewa malalata - Kungiyar kare hakkin musulmai ta kare Buhari

Atiku ma ya taba cewa ‘yan arewa malalata - Kungiyar kare hakkin musulmai ta kare Buhari

- Kungiyar sanin kula da hakkin musulmai (MURIC) ta bayyana cewa kalaman shugaba Buhari game da matasan Najeriya daidai ne

- Jawabin wanda shugaban kasa Buhari yayi a taron Commonwealth Business Forum a Westminster, shugaban yace wasu daga cikin matasan Najeriya basuje makaranta ba amma suna jiran kudin mai

- Jawabin wanda a kawo cece kuce sosai a kafar sadarwa ta yanar gizo, wanda har akayiwa take da ‘LazyNigerianYouth’

Kungiyar sanin kula da hakkin musulmai (MURIC) ta bayyana cewa kalaman shugaba Buhari game da matasan Najeriya daidai ne.

Jawabin wanda shugaban kasa Buhari yayi a taron Commonwealth Business Forum a Westminster, a ranar Laraba, shugaban yace wasu daga cikin matasan Najeriya basuje makaranta ba, amma suna jiran kudin mai.

Jawabin wanda a kawo cece kuce sosai a kafar sadarwa ta yanar gizo, wanda har akayiwa take da ‘LazyNigerianYouth’, wanda ya kawo rudani da dama a tsanin mutane.

Atiku ma ya taba cewa ‘yan arewa malalata - Kungiyar kare hakkin musulmai ta kare Buhari
Atiku ma ya taba cewa ‘yan arewa malalata - Kungiyar kare hakkin musulmai ta kare Buhari

A wani jawabi da aka fitar ranar Litinin, Ishaq Akintola, Daraktan kungiyar, yace Buhari ba shine shugaba na farko a Najeriya da ya fara kiran mutane malalata ba.

KU KARANTA KUMA: Saraki da Tambuwal bazasu bar APC ba - Gwamna Badaru

Ya lissafo “tsohon mataimakin shugaban kasa nan Atiku Abubakar; Gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson; Tsohon shugaban kasa na lokacin Soja, Ibrahim Babangida, duk sun kira ‘yan Najeriya malalata, amma na shugaba Buhari kadai ya zama laifi”, inji shi.

A halin yanzu, tsohon shugaban kasar Ghana ya nisanta kansa da maganar da shugaba Buhari yayi game da matasan Najeriya.

A jawabin da aka fitar daga Ofishin Rowlings ta hannun Kobina Andoh Amoakwa, ya bayyana cewa shi baiyi wani jawabi ba game da jawabin shugaba Buhari akan matasan Najeriya cewa duk karya ne maganganun da ake yadawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng