Tantamar ko Saddam Hussaini yana raye, an tona kabarinsa ba'a ga gawar sa ba
- An nemi gawar Saddam Husseini an rasa
- Shekara 12 bayan mutuwarshi, ina gangar jikin Saddam?
- Ko dai bai mutu ba?
Saddam Hussain ya yi shugabancin kasar Iraq da 16 ga watan yuli 1979 zuwa 9 ga watan Afirilu 2003. Ya mulki Iraq da tsantsaini. Mabiyanshi suna cewa mulkin shi shi ya kai Iraq inda take a yanzu ta fuskar wayewa da tattalin arziki.
Marasa goyon bayan shi kuwa cewa sukayi shugabane shi mara tausayi. Baya da haka ya samu nasarori da dama a mulkin shi ta hanyar juya kasar yanda yaso ko a lokacin yakin sojoji.
Shuwagabanni da suna rayuwarsu ne cikin jindadi kuma ba wanda zai yi tsammanin zasu yi karshe mara kyau. An yanke ma Saddam Hussain hukuncin daurin rai da rai a wata kotun Iraq bayan an kama shi da laifin da suka sabawa doka da kuma kashe 'yan shi'a 148.
A ranar 30 ga watan Disamba 2006 ne aka rataye kasaitaccen shugaban Iraq. A washegarin ranar ne aka kai gawarshi mahaifarshi kusa da Al Awjah.
A wannan lokacin ne shugaban kasa Amurka George Washington Bush ya bada umarnin daukar gawar Saddam Hussain daga Baghdad zuwa Tikrit a jirgin sojojin Amurka,a inda aka birne gawarshi a Mausoleum.
DUBA WANNAN: Hadari ya rutsa da matan Chibok
Bayan birne shi ne ake kaiwa kabarin shi ziyara duk 28 ga Afirilu na kowacce shekara saboda itace ranar haihuwar shi. A inda dubban mabiyanshi wanda suka hada da dalibai suke ziyartar kabarin shi.
A yanzu dai akwai jita jita kala daban daban da tace an sace gawar Saddam daga kabarin shi ko kuma dama ba a rataye shi bane? Mene ne gaskiyar zancen?
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng