Anyi wani kazamin karon batta tsakanin sojin Najeriya da ‘yan Boko Haram, an rasa rayuka a kowanne bangare

Anyi wani kazamin karon batta tsakanin sojin Najeriya da ‘yan Boko Haram, an rasa rayuka a kowanne bangare

- A daren asabar ne aka yi wata fafatawa tsakanin dakarun sojin Najeriya da mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno

- Sojojin Najeriya uku, Civilian JTF biyu da mayakan kungiyar Boko Haram uku ne suka mutu yayin musayar wuta tsakanin bangarorin biyu

- A sanarwar da kakakin hukumar Soji, Texas Chukwu, ya fitar t ace, mayakan Boko Haram ne suka fara kaiwa wani sansanin dakarun sojin hari

Hukumar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wasu jami’an ta uku dake rundunar Ofireshon Lafiya Dole da wasu mambobin kungiyar agaji ta farin hula uku a wata musayar wuta tsakanin jami’an tad a mayakan kungiyar Boko Haram a jiya, Asabar.

Hukumar sojin t ace ta fara cin karo ne da wasu mata da kananan yara yayin wani samame da ta kai wata mafakar mayakan kungiyar ta Boko Haram kuma suka amsa cewar iyalan mayakan kungiyar ‘yan ta’addan ne.

Anyi wani kazamin karon batta tsakanin sojin Najeriya da ‘yan Boko Haram, an rasa rayuka a kowanne bangare
Anyi wani kazamin karon batta tsakanin sojin Najeriya da ‘yan Boko Haram, an rasa rayuka a kowanne bangare

A wata sanarwa da darektan hulda da jama’a a hukumar soji, Birgediya Janar Texas Chukwu, ya fitar ta ce, mayakan kungiyar Boko Haram ne suka fara kai hari kan jami’an hukumar na runduna ta 25 dake aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno karkashin atisayen Ofireshon Lafiya Dole.

DUBA WANNAN: Kun jawowa Najeriya asara, Sarki Sanusi II ya caccaki ministocin Buhari

Bayan ta ci galabar mayakan kungiyar, hukumar sojin t ace tayi nasarar kama wasu makaman ‘yan ta’addar da suka hada da; bindigu cike da harsashi, bindiga mai farfela, alburusai da sauran su.

Hukumar sojin ta shawarci jama’a das u sanar da duk wani motsi da suka gani a yankunan su da basu yarda das hi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel