Rigimar Larai da Farsi: Muna iya kaca-kaca da dukkan biranen Saudiyya in mun so, cikin awanni'

Rigimar Larai da Farsi: Muna iya kaca-kaca da dukkan biranen Saudiyya in mun so, cikin awanni'

- Tun bayan mutuwar annabi ake rigima tsakanin Shi'a da Sunna a duniya

- Su shi'a sun koma gabas da kuma arewa, watau Iran da Iraqi don jiran 'ranar tumbuke masu kwace'

- Su kuma Sunni sun ce addini da siyasa sai an raba su, sun hana ahlul-baitin mulki

Rigimar Larai da Farsi: Muna iya kaca-kaca da dukkan biranen Saudiyya in mun so, cikin awanni'
Rigimar Larai da Farsi: Muna iya kaca-kaca da dukkan biranen Saudiyya in mun so, cikin awanni'

Kasar Iran, wadda bata ga-maciji da kasar Saudiyya, tayi barazanar kakkabe dukkan biranen kasar Saudiyya daga doron kasa, muddin kasar ta Saudiyya ta sake tsoma baki ko karadin wai zasu yi yaki da juna a nan gaba.

Kalaman na zuwa ne daga bakin Janar na kasar ta Iran, Redha Kharam Tussi, wanda shine kwamandan sojin gani-kasheni na kasar ta Farisa, watau Republican Gurads na ita kasar ta Persia mai dumbin tarihi.

Kasashen dai sun shekara 1400 suna yakin ruwan sanyi da na zafi, saidai tun daga juyin juya halin 1979, wanda Limamin shi'ar Khomaini ya faro, da sunan ahlul baiti, fadan ya sake zafafa, musamman bayan da ya kira kansa jikan annabi, kuma yayi kira da a tumbuke Ahl Saud daga mulkar 'biranen Islama.'

Su kuwa larabawa suka ingiza Saddam Hussain ya yaki kasar ta Iran a 1980-1988, inda shima yace ai shima jikan annabin ne. Da taimakon turawan yamma, wadanda kuma suka zagaye suke baiwa Iran din makamai, duk da suna baiwa Iraqi a bayyane.

A 2011, larabawa suka tashi suka fara hambaras da nasu shuwagabannin, kasashen biyu kuwa suka fara yakar juna ta hannun kananan kasashe da suke da iko dasu, kamar Yemen, Lebanon, da Siriya da ma Iraki.

DUBA WANNAN: Sai ga Jonathan a 2015 yana yabon 'lalacin samari' a sabon bidiyo

A Najeriya ma, an sha gwabzawa tsakanin samarin Sunna da Shia, inda kowannensu ke ikirarin shine musulmi dayan kafiri, a siyasar da suka dauka ta shafe su, har sukan kashe juna bayan kafirta juna.

Kalaman Janar Redha Kharam Tussi din dai, na zuwa ne bayan da Yarima Salman ya saki baki da cewa yana sa rai cikin nan da shekaru 10 zuwa 15 yana sa rai za'a yi fadan gaba-gaba tsakanin kasar tasa da kasar Iran.

Redha Kharam Tussi yace: "Ina yi wa shugabannin Saudiyya hannunka-mai-sanda game da tsokanar fitina da kuma furta kalaman wuce gona da iri. Baku da karfi da kuma isassun makaman da zaku yi tinkaho da su. Awanni 48 kacal sun ishe mu yin kaca-kaca da kasarku. Shi yasa ku rufe bakunanku ku zauna.."

A baya dai a tarihi, tsakanin wadannan dauloli, na ahlul-baiti masu bin Ali, da na Sahabbai masu bin su Abubakar, sun sha gwabzawa, wasu lokutan harda iyalan annabi da matayensa.

Wannan basasa ta faro ne bayan da shi annabin na musulmi ya fasa mika mulki ga abokansa, yace Aliyu da jikokinsa su Hassan da Husaini sune zasu yi mulkin siyasa da addini, watau Imami/Khalifa, lamari da ya janyo 'juyin mulkin Umar' bayan da annabin yayi wafati.

A yau dai, ko a kasar zariya, Kano da Sokkoto, samari kan iya kashe junansu kawai don wasunsu sun bi wani bangare na wadancan larabawa da farisawa dake fada tsakaninsu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel