PDP 2019: Sai ga Jonathan da Malam Ibrahim Shekarau, ko wacce waina suke toyawa?

PDP 2019: Sai ga Jonathan da Malam Ibrahim Shekarau, ko wacce waina suke toyawa?

- A baya da Malam IbrahiShekarau aka kafa jam'iyyar APC

- Sai dai jam'iyyar ta zamo ta masu neman takara daga PDP in gwamna Kwankwaso ya shiga

- Malam din yayi abin da ba'a zata ba, inda ya shiga jam'iyyar da ya kira ta 'banza-a-banza'

PDP 2019: Sai ga Jonathan da Malam Ibrahim Shekarau, ko wacce waina suke toyawa?
PDP 2019: Sai ga Jonathan da Malam Ibrahim Shekarau, ko wacce waina suke toyawa?

Tun bayan da suka fadi zabe a 2015, shugab Jonathan da tsofin ministoci/gwamnoninsa, ke ta sake-saken yadda zasu dawo kan mulki, ko kuma su dora nasu musamman ganin yadda abokansu ke cikin ha'ula'i na kame da bincike da kwacen kudaden da ake sa rai ta haramun aka samo su.

A irin wannan ne, sai aka hango Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, kuma tsohon Ministan ilimi, a Yenogoa, babban birnin jihar Bayelsa, mahaifar tsohon shugaban na Najeriya GEJ.

A baya dai Mal. Ibrahim Shekarau yayi takarar shugabanci kasar nan a 2011, karkashin jam'iyyar ANPP, inda shi kuma shugaba Buhari yayi takara a CPC, inda ake ganin kamam cin amana ne bayan a 2003 tare suka fafata da PDP din a ANPP.

DUBA WANNAN: Sai ga Jonathan yana yabon samari

A gari an ga fasta ta Malamin Gwamnan mai nuna alamar yana sansanar kujerar shugaba Buhari, kuma an san har yanzu basu ga-maciji da tsohon gwamnan Kanon Dr. Rabiu Kwankwaso, Sanata na yanzu, wanda ya koma APC.

A sabon tsarin dai, ana sa rai, ko Malamin yayi takara, ko ya zugo GEJ din yayi takara, ko kuma su hada kai su mara wa Atiku Abubakar baya domin kayar da APC daga mulki.

In kuma da Malaminn yaso, zai iya neman ujerar Sanata Kwankwaso, watau Santan Kano ta tsakiya, su farfado da gabarsu ta shekaru 17.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel