Tsakar daren jiya 'yan bindiga suka far ma wasu kauyukan Binuwai, sun kashe akalla 10
- Matsalar dai har yanzu ta kabilanci ce, watau makiyaya da manoma
- Ta rikice ta zama ta ramuwar-gayya da cin zali
- Gwamnati ta girke bataliyoyi, amma a banza
A daren jiya ne aka sake samun tashin hankali a jihar Benue, jiha da har yau ake ta samunn kashe-kashe da suka shafi kabilanci da kisan kare dangi, wanda aka fi dangantawa da makiyaya-manoma, wanda ya rutsa fda fulani masu kiwo da masu ta'addanci.
A kashe-kashen, da kone konen, an kashe akalla mutane 10, an kuma jikkata da dama, wasu kuma tuni suka tsere gudun hijira daga yankin Guma, Saghev, Tse-Abi, Tse-Ginde, Tse-Peviv, Tse-Ikyo, Agenke da Gbenke.
DUBA WANNAN: Hasashen 2019: APC a yankin Yarabawa
Bayanan sun fito ne ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar Ortom, Terver Akase, kuma ya ta'allaka hare-haren da cewa Fulani ne suka kai shi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng