Gangamin Tazarce: Jirgin Buhari 2019 ya isa kasashen Ibo

Gangamin Tazarce: Jirgin Buhari 2019 ya isa kasashen Ibo

- Kabilar Ibo basu fiye wani son Buhari ba

- A yankin ne masu adawa dashi suke sa rai zasu kayar dashi a 2019

- Lissafin APC shine zawarcin manyansu, ko sa hado kuri'un da ake bukata

Gangamin Tazarce: Jirgin Buhari 2019 ya isa kasashen Ibo
Gangamin Tazarce: Jirgin Buhari 2019 ya isa kasashen Ibo

Tun dai da aka yi yakin basasar kasar nan, sojojin Arewa basu fiye karbuwa a wurin kabilar Ibo ba, musamman yanzu da kabilancin ya dawo gadan-gadan.

Shi dai shugaba Buhari a 2015 ya kayar da Ebele Jonathan, mafi kusanci ga ulkin Ibo, wanda basu taba samu ba tunn Alex Ikweme da yayi mataimakin shugaba Shagari a 1979, Janar Ironsi kuma yayi ne tun bayan tumbuke su Tafawa Balewa a 1966.

A yanzu dai APC jam'iyya mai mulki na kokarin ganin ta hado kan kabilun yankkin domin cinye zaben 2019, inda ake sa rai jam'iyyun Adawa ne zasu lashe zaben yankin.

DUBA WANNAN: Shawagin karshe na CHOGM

Ofisoshin Kamfe na shugaba Buhari zasu bude kamfe a yankunan, inda zasu ara da kabilun da ke kusa da Ibon, amma kuma ba Igo din bane, domin dai rara-gefe kafin a shiga kamfe gadan-gadan,

Jihohin da suke hari a yanzu, inda za'a bude ofisoshin, sun hada da Edo, Akwa Ibom da kma Cross Rivers.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel