Wasu kungiyoyi 20 sun zabi Bafarawa a matsayin dan takarar shugabancin kasa
Wasu kungiyoyin arewa 20 wanda suka hada da kungiyoyin mata da na matasa a fadin yankin Arewa maso yamma sun dauki alkawarin siya wa tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa fom din takarar zaben shugabancin kasa a 2019.
Kungiyoyin sun yanke wannan shawarar ne bayan wani taro da suka gudanar a garin Kaduna karkashin wata kungiya mai suna 'Bafarawa Initiative for Peace, Unity and Progress', sun kuma yi alkawarin yin tattaki zuwa gidan tsohon gwamnan don su tursasa masa ya fito takarar.
Shugaban kungiyar, Alhaji Abdullahi Mu'azu yace, "Zamu tattaro miliyoyin matasa mu tafi zuwa gidan Bafarawa a Sakkwato don mu bukaci ya fito takarar shugabancin kasar a shekarar 2019."
KU KARANTA: Kalubalen tsaro guda 5 dake cinma shugaba Buhari tuwa a kwarya
Ya kuma ce Attahiru Bafarawa dan siyasa ne mai zon zaman lafiya, aiki tukuru, kuma yana daraja matasan Najeriya fiye da shugaba Muhammadu Buhari. Ya kara cewa babu wani gwamna da ya aiwatar da ayyukan cigaba a tarihin jihar Sakkwato kamar Bafarawa.
A bangarensa, mai magana da yawun tsohon gwamnan jihar Sakkwaton, Mallam Yusuf Dingyadi yace Bafarawa zai yi nazari akan bukatar da kungiyoyin suka mika masa kuma ya duba halin da kasar ke ciki sanan ya bayar da amsa.
Dingyadi kuma yace an dade ana ta yin kira ga tsohon gwamnan ya fito takarar shugabancin kasa a Najeriya amma har yanzu yana nazarin ne kuma yana addu'a Allah yayi masa zabi na alheri a kan lamarin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng