Ku tabbata kun zabi 'Yan takara Nagari - Shehi Dahiru Bauchi ga Al'ummar Najeriya

Ku tabbata kun zabi 'Yan takara Nagari - Shehi Dahiru Bauchi ga Al'ummar Najeriya

Jagoran 'Darikar Tijjaniya Shehi Dahiru Usman Bauchi, ya gargadi daukacin al'ummar Najeriya akan zaben 'yan takara nagari a yayin kada kuri'un su a zaben 2019.

Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai a Jihar Bauchi inda yake jawabai dangane da bikin Maulidin Shehi Ibrahim Inyass da aka gudanar a babban birnin kasar nan na tarayya da kuma jihar Kaduna.

Yake cewa, al'ummar Najeriya su tabbata sun kada kuri'un su ga 'yan takara nagari da za su bayar da dama ta sharbar romon dimokuradiyya.

Jagoran 'Darikar Tijjaniyya na Najeriya; Shehi Dahiru Bauchi
Jagoran 'Darikar Tijjaniyya na Najeriya; Shehi Dahiru Bauchi

Shehin na Bauchi ya kuma tabbatar da cewa, dimokuradiyya ta bayar da dama ga kowace al'umma wajen kada kuri'u ga 'yan takara da suka dace da zaɓin ta, inda ya nemi al'ummar Najeriya akan su tabbata sun mallaki katin zabe domin shine 'yancin su.

KARANTA KUMA: Ba bu wani tallafi na agaji da Hukumar NEMA ta bamu - Geidam

A kalaman Shehi, "wasu mutane su kan ce kuri'unku su ne 'yancin ku sai dai ni a nawa bangaren kuri'un ku su ne makaman ku. Saboda haka ya rage ga mutum ya zaɓi wanda zai hallaka shi ko kuma jagoranci nagari."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel