Gwamna Geidam ya ware N300m don wani aikin farantawa ma'aikata a jiharsa

Gwamna Geidam ya ware N300m don wani aikin farantawa ma'aikata a jiharsa

- Gwamnatin jihar Yobe ta rabawa ma'aikata bashin kayan kafinta na Naira miliyan 300

- Shugaban ma'aikatan jihar Saleh Abubakar ya bayyana cewa anyi hakan ne don ma'aikatan su amfana

- Kamar yanda yace, basu sa ma ma'aikatan riba ba akan bashin Naira miliyan 300 wanda ake tsammanin zasu biya cikin watanni 25

Gwamna Geidam ya ware N300m don wani aikin farantawa ma'aikata a jiharsa
Gwamna Geidam ya ware N300m don wani aikin farantawa ma'aikata a jiharsa

Shugaban ma'aikatan jihar Yobe, Saleh Abubakar ya bayyana cewa anyi hakan ne don ma'aikatan su amfana.

Kamar yanda yace, basu sa ma ma'aikatan riba ba akan bashin Naira miliyan 300 wanda ake tsammanin zasu biya cikin watanni 25.

"Wannan bashin na kayan kafinta ya zagaye kowa amma duk wanda bai samu ba an amince za a gyara mishi gidan shi a kowane guri yake a jihar" Abubakar yace.

Ya kara bayyana cewa bashin mataki mataki ne, zababbun shuwagabannin ma'aikatu sun samu miliyan dai dai,ma'aikatan masu mataki 1 zuwa 5 sun samu 50,000.

Bayan haka kwamitin shugabancin kasa na wayar da kan arewa maso gabas da hadin guiwar Gwamnatin jihar Yobe zata horar da malamai 372.

Ta'addancin da ya faru a 2012 ya lalata makarantu tare da wargaza da tsoratar da malaman jihar.

DUBA WANNAN: Farashin mai a duniya a yau

A yayin da take magana da malaman a Damaturu, shugaban horar da malaman Faith Anifowoshe tace an shirya taron horarwan na kwana biyar ne don karfafa malaman da abin ya shafa.

A farkon shekarar 2018 kwamitin PCNI ta horar da malamai a jihar da suke makwaftaka, Adamawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng