Abin takaici: Wani Magidanci ya sumar da kanwarsa bazawara saboda ta hau bishiyar Mangwaro

Abin takaici: Wani Magidanci ya sumar da kanwarsa bazawara saboda ta hau bishiyar Mangwaro

Kaico! Wani abin kunya, abin takaici ya faru a gidan Narabi a kauyen Kugu da ke gundumar Dutsen Abba, a cikin karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna, inda wani Magidanci ya lakadan ma kanwarsa da suke Uba daya dukan kawo wuka saboda ta tsinki mangwaro.

Aminiya ta ruwaito wannan mata da ta sha da kyar mai suna Huwaila Abubakar daga gadon Asibitn da take kwance tana jiyar lahanin da dan uwanta yayi mata, tana ba cas ba as dan uwan nata ya tafka mata wannan ta’asa.

KU KARANTA: Cikin naira biliyan 4, EFCC ta kwato naira miliyan 473 daga hunnun jigon APC

“Da misalin karfe 3 na ranar Asabar na dauko makata don na tsinko wani mangwaro nunanne da na hango a bishiyan gidan Yayana, ina tsinkowa sai kawai ya fado a kan kwano, kwatsam sai yayana mai suna Isa ya fito ya hauni da bugu, inda ya farfasa min baki har sai da na suma.” Inji ta.

Abin takaici: Wani Magidanci ya sumar da kanwarsa bazawara saboda ta hau bishiyar Mangwaro
Huwaila

Sai dai Huwaila ta shaida ma majiyar Legit.ng cewa dama can yan dakinsu yayan nata basa kaunar yan dakinsu sakamakon zargin cewa wai Mahaifinsu ya fi kaunarsu, kuma su biyu rak a dakinsu, duka mata, inda tace zaman hakuri suke yi da juna na tsawon lokaci.

Huwaila ta bayyana cewa a sanadiyyar mutuwar mijinta ya sanya ta koma gida da zama har wannan lamari ya sameta, amma ta ce ta yafe masa, duk da cewa tuni Yansandan yankin suka kama yayan nata, kamar yadda babban jami’in ofishin Yansanda na Dan Magaji, Buhari Bello ya tabbatar.

Shi ma mahaifinsu, Malam Abdullahi Maibindiga ya bayyana damuwarsa da bacin rai game da lamarin, inda yace ya sha jan hankalinsu game da irin kiyayyar dake tsakaninsu, inda ya bukaci hukuma ta dauki matakin daya dace, ko kuma shi yayi dauki matakin da ya dace.

Daga karshe shugaban Asibitin da aka kwantar da Huwaila, Dakta Nura Hashim ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace su suka duba Huwaila a lokacin da aka kawo ta cikin mawuyacin hali a ranar Asabar din da ta gabata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng