Dandalin Kannywood: Allah ya azurta Rahma Hassan da ýa mace (hoto)
Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa Allah ya azurta tsohuwar jarumar nan ta Kannywood, Rahama Hassan da haihuwa.
Ta bayyana hakan ne a shafints na sada zumunta inda ta sanar da cewa Allah ya bata haihuwar ýa mace.
Ga abunda ta rubuta a shafin nata: "Alhamdulillah.
“Ina mai farin cikin sanar da ku Allah ya azurta mu da 'ya mace.
KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya bazasu sake yarda suyi gwamnatin talauci ba – Tsoffin yan bindiga ga Buhari
“Ina nema mata kyawawan addu'o'inku domin ta kasance cikin 'ya'ya nagri masu albarka wacce za ta taimaki al'ummarta da addininta.”
Ga hoton a kasa:
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng