Za a samu habakar tattalin arziki da kashi 3.6% a 2019-20 a irin su Najeriya

Za a samu habakar tattalin arziki da kashi 3.6% a 2019-20 a irin su Najeriya

- Babban bankin Duniya yace za a ga kasuwar tattalin arziki a Najeriya

- Har Kasashen Afrika irin su Angola da Afrika ta Kudu suna cikin sahun

- Sai dai kuma an ce sai Kasashen sun yi a hankali kar su koma gidan jiya

A tsakiyar makon nan ne Babban bankin Duniya ya bayyana cewa ba mamaki tattalin arzikin Najeriya da wasu kasashen ya kama hanyar habaka cikin 'yan shekaru masu zuwa. Daga cikin wannan kasashen dai akwai Kasar Afrika ta Kudu.

Za a samu habakar tattalin arziki da kashi 3.6% a 2019-20 a irin su Najeriya

Tattalin arzikin Najeriya yana habaka inji bankin Duniya

A ranar Laraba dinnan ne da aka yi wani babban taron da aka saba na rabin shekara inda babban bankin ya bayyana lallai za a ga cigaba a habakar tattalin arzikin kasashen Afrika da kewaye a shekarar nan ta 2018 har zuwa shekarar 2020.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta yi tafka da warwarwa kan harkar man fetur

Haka zalika bankin Duniyan na mai cewa daga badi watau 2019 zuwa 2020 kuma za a samu habaka na kashi 3.6% a Kasashe irin su Najeriya da Angola da kuma Kasar Afrika ta Kudu wanda su ka fi kowane kasa karfin Nahiyar.

Sai dai duk da cigaba da ake samu wani babban Jami'in bankin a Yankin Afrika Albert Zeufack yace sai Kasashen sun yi ta-ka-tsan-tsan gudun a koma gidan jiya saboda rashin karfin kasashen da kuma rashin raba kafa a harkar tattali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel