'Dan Najeriya 1 na mutuwa cikin kowane minti 2 - Likitar Kwakwalwa
A wani sabon nazari gami da binciken wata kwararriyar a fannin kiwon lafiya Farfesa Njideka Okubadejo ta yi hasashen cewa, cikin kowane minti biyu ana samun dn Najeriya daya da yake rasa rayuwar sa a sakamakon bugun zuciya.
Farfesa Njideka wadda ita ce mace ta farko a duk fadin Najeriya da ta karatun a fannin nazarin kwakwalwa ta bayyana hakan ne a yayin gudanar da wata lacca a jami'ar jihar Legas.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, kimanin mutane 120 zuwa 240 ke mutuwa cikin kowane adadin mutane na 100, 000 sakamakon bugun zuciya.
Farfesan dai ta bayyana cewa, bugun zuciya cuta dake afkuwa a yayin da jini ya daina kaiwa zuwa ga wani ɓangare na kwakwalwa ba bu zato ba tsammani.
A yayin da kwayoyin halittu na cikin kwakwalwa suke dogaro da sunadarin Oxygen na cikin jini, wannan lamari ka iya janyo mutuwar kwayoyin halittu na kwakwalwa cikin 'yan sa'o'i kadan.
KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Neja za ta dauki matasa 500 aiki domin rage zaman banza
Ta kuma yi fashin bakin dangane da wasu hanyoyi biyu dake haddasa bugun zuciya, inda hanya ta farko ke kasancewa a yayin da kwayoyin cuta suka datse tashoshin jini masu kaiwa ga kwakwalwa.
Hanya ta biyu kuma ita ce fashewar magudanan jini ko kuma digar tashoshin jini a yayin kaiwa ga kwakwalwa sakamakon matsi ko takura.
Kwararriyar likitar ta kuma yi karin haske kan ababe dake haddasa wannan cuta inda ta bayar da su kamar haka: ciwon suga, hawan jini, ta'ammali da barasa, sigari, muggan kwayoyi, shan magunguna ba tare da lura ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng