Matsalar tsaro: Buhari zai hada taron gaggawa

Matsalar tsaro: Buhari zai hada taron gaggawa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bude taron yankunan kasar nan a Abuja tsakanin 26 zuwa 29 ga watan Afirilu don kawo karshen kashe kashen da makiyaya ke yi a kasar

- Ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau ya bayyana hakan ga manema labarai a gidan gwamnati jiya. Yace Gwamnatin tarayya ta damu da matsalar da ake samu tsakanin makiyaya da manoma

Matsalar tsaro: Buhari zai hada taron gaggawa
Matsalar tsaro: Buhari zai hada taron gaggawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bude taron yankunan kasar nan a Abuja tsakanin 26 zuwa 29 ga watan Afirilu don kawo karshen kashe kashen da makiyaya ke yi a kasar.

Ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau ya bayyana hakan ga manema labarai a gidan gwamnati jiya. Yace Gwamnatin tarayya ta damu da matsalar da ake samu tsakanin makiyaya da manoma.

DUBA WANNAN: Kamfanin Shell zai saka hannun jarin Dala Biliyan 15 a Najeriya - Shugaba Buhari

Dambazau yace ma'aikatar shi ce ta kirkiro da taron wanda zai zo karkashin kungiyar hadin kan kasashen Afirika ta yamma ECOWAS na dokar su.

Yace taron zai hada ministocin da suke ta bangaren tsaro da noma a kasashen 15 na ECOWAS da wasu kasashen tsakiyar Afirika.

"Amfanin taron shi a duba matsalar kaiwa da kawowa tsakanin kasa da kasa. Misali, kowanne mutum in zai shiga wata kasa Dole ne ya sanar da hukumar kasar da yaje sannan yaje da shaidar cikakkiyar lafiyar shanun da zai je dasu."

"saboda haka in mutum a Misali ya shiga kasa da shanaye 10 kuma aka ganshi zai fita da guda 20 Dole a tuhumeshi saboda gudun satar shanun. Sannan Dole mu tabbatar da cewa dabbobin da aka shigo dasu basu da wata cuta. "

" Sannan kuma dole a kiyaye dokokin kasa da kasa. Da kuma maganar daukan makamai, bazamu aminta da hakan ba" inji shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng