Hukumar EFCC zata gurfanar da Sanata Kwankwaso da Wamako

Hukumar EFCC zata gurfanar da Sanata Kwankwaso da Wamako

- Tsofafin gwamnoni wadanda a yanzu suke majalisar dattawa a karkashin jam'iyya mai mulki yanzu APC zasu amsa gayyatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa tayi musu

- Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso (APC, Kano) da Aliyu Magatakarda Wamakko (APC, Sokoto) zasu amsa tambayoyi akan zargin da ake musu na almundahanar kudi da barnatar da kudin jihar su a lokacin mulkin su

Hukumar EFCC zata gurfanar da Sanata Kwankwaso da Wamako

Hukumar EFCC zata gurfanar da Sanata Kwankwaso da Wamako

Tsofafin gwamnoni wadanda a yanzu suke majalisar dattawa a karkashin jam'iyya mai mulki yanzu APC zasu amsa gayyatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa tayi musu.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso (APC, Kano) da Aliyu Magatakarda Wamakko (APC, Sokoto) zasu amsa tambayoyi akan zargin da ake musu na almundahanar kudi da barnatar da kudin jihar su a lokacin mulkin su.

DUBA WANNAN: 2019: Kabiru Turaki ne ya dace da kujerar shugabancin kasar nan a jam'iyyar PDP - inji Dattawan Arewa

A lokacin da Kwankwaso za a gayyace shi akan zargin kwashe kudin kananan hukumomi har Naira biliyan 3.8, shi kuma tsohon gwamnan Sokoto za a bukaci da ya warware zargin da ake mishi na satar kudin al'umma da almundahanar kudi Naira biliyan 15.

Majiyar mai karfi daga hukumar ta sanar da Legit.ng jiya, cewa hukumar a halin da ake ciki tana kara bincike akan zargin da Sanatocin na APC a 2015.

Inji Majiyar tace gayyatar Kwankwaso da za ayi zai biyo bayan karar shi da aka kawo ne ga hukumar wanda Barrister Mustapha yasa hannu a maimakon Engineer Abubakar Maisha'ani da Alhaji Najumai Garba Kobo.

A karar mai kwanan wata 27 ga watan Mayu, 2015. Sanata Kwankwaso ya karbi Naira miliyan 70 daga kananan hukumomi 44 na jihar wanda jimillar shi ta kama Naira biliyan 3.08 a gabannin zaben fidda gwani na Shugaban kasa a 2015.

Hukumar zata gayyaci Sanata Wamakko akan karar da wata kungiya mai suna "Movement for the Liberation and Emancipation of Sokoto State" ta kawo mai kwanan wata 10 ga watan Augusta, 2015 da sa hannun shugaban karamar hukuma, M.D Sirajo da sakatare, Mudashiru Umar Alhassan na zargin shi da akeyi da handame kudi har Naira biliyan 15 tsakanin 2011 da 2015.

Mai magana da yawun hukumar yaki da rashawa yace tabbas hukumar na bincike akan zargin da ake wa sanatocin guda biyu kuma nan ba da dadewa ba za a kira su don kare kansu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel