Shahararren tsohon dan kwallon Najeriya ya nemi hadin kan Sheikh Pantami game da ayyukan cigaba

Shahararren tsohon dan kwallon Najeriya ya nemi hadin kan Sheikh Pantami game da ayyukan cigaba

- Kanu Nwankwo ya kai ma Sheikh Pantami, shugaban NITDA ziyara

- Dan Kwallon ya nemi hadin kan hukumar NITDA wajen ceton rayukan kananan yara

Tsohon shugaban yan wasa na kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Kanu Nwankwo ya jinjina ma shugaban hukumar cigaban ilimin kimiyya da fasaha, NITDA, Sheikh Isa Ali Pantami kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Kanu yayi wannan jinjin ga Pantami ne a ranar Laraba 18 ga watan Afrilu a yayin wata ziyara da ya kai masa a babban ofishin NITDA dake garin Abuja, inda yace Pantami ya cancanci yabo sakamakon yadda ya sauya fasalin NITDA, ta zamo hukumar gwamnati guda daya tilo da tafi ingaci.

KU KARANTA: Yawanci matasan Najeriya basu son karatu, sun fi kaunar zaman kashe wando – Buhari daga Landan

Shahararren tsohon dan kwallon Najeriya ya nemi hadin kan Sheikh Pantami game da ayyukan cigaba
Kanu da Malam

Kanu ya nemi kulla alaka tsakanin NITDA, gidauniyarsa ta Kanu Heart Foundation dake kula da kananan yara masu ciwon zuciya, don taimaka ma ire iren yaran dake fama da wannan cuta.

A nasa jawabin, Dakta Ali Pantami ya yaba da kokarin da gidauniyar Kanu ke yi wajen jajircewar da ta nuna na ceton rayuwar kananan yara masu ciwon zuciya, ba tare da nuna bambamcin addini ko kabila ba.

Shahararren tsohon dan kwallon Najeriya ya nemi hadin kan Sheikh Pantami game da ayyukan cigaba
Ziyarar

“Ina matukar girmama tare da ganin duk wani mutumin dake ceton rayukan mutane da kima.” Inji Sheikh Isa Ali Pantami, shugaban hukumar cigaban ilimin kimiyya da fasaha, NITDA.

Shahararren tsohon dan kwallon Najeriya ya nemi hadin kan Sheikh Pantami game da ayyukan cigaba
Ziyarar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng