Alhaki dan kwikwiyo ne: Babbar Kotu ta tumbuke mataimakin Kaakakin majalisar dokoki
Wata babbar Kotun jihar Delta dake zamanta a garin Kwale, cikin karamar hukumar Ndokwa ta yamma ta tumbuke mataimakin Kaakakin majalisar dokokin jihar Deelta, Friday Osanebi, inji rahoton Daliy Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kotun ta baiwa mataimakin Kaakakin majalisar mamaki ne sakamakon kama shi da laifin amfani da takardun karatu na bogi a kokarinsa na zaman dan majalisar dokokin jihar.
KU KARANTA: Toh fa! Shehu Dahiru Bauchi ya tabbatar tare da gaskata bayyanar Inyass a fitilar kan titin Abuja
Wani abokin takarar dan majalisar ne da ya fito daga jam’iyyar PDP, Emeka Odegbe ne ya shigar da shi kara gaban Kotun, inda ya zargi dan majalisar da amfani da takardun bogi wajen cika burinsa na zama dan majalisa, tun daga zaben cikin gida na jam’iyyar PDP, wanda yace hakan bai kamaci dan majalisa ba, don haka ya bukaci Kotu ta sanar da shi a matsayin halastaccen dan majalisa.
Alkalin Kotun, Mai shari’a V.I Ofezi ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta yi maza maza ta janye shaidar lashe zabe da ta baiwa Osanebi, kamar yadda wanda ya shigar da karar, Emeka Odegbe ya bukata.
Dayake ba’a nan gizon ke sakar ba, Alkalin Kotun ya kara umartar INEC ta mika ma Emeka sabuwar shaidar lashe zaben kujerar dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar Ndokwa ta yamma, a matsayinsa na halastaccen dan takarar jam’iyyar PDP a wannan zabe.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng