2019: Dalilai 5 da suka sa nake yiwa Buhari yakin neman zabe - Babban lauya Keyamo

2019: Dalilai 5 da suka sa nake yiwa Buhari yakin neman zabe - Babban lauya Keyamo

Shararen lauya mai kare hakkin dan adama, Festus Keyama (SAN) ya bayar da dalilai biyar da suka sanya ya amince yayi wa shugaba Muhammadu Buhari aiki a matsayin kakakin yakin neman zabe na 2019. Ga dalilan nasa a kamar haka;

1) Yaki da rashawa

Ya bayyana a tarihin nigeriya babu wata gwamnati da tayi kokari wajen nemo kudaden kasar sama da shugaba Muhammad Buhari. Wannan shine dalilin zabarsa domin kare talakawan kasar mu. Wannan yana daya daga cikin dalilan da yasa nake alfahari dashi kuma nake kokarin sake zabarsa.

A yayin da nake aiki tare da maigida na marigayi Cif Gani Fawehinmi (SAN) wanda shi ya bani shawara a lokacin da yake raye babu gwamnatin da yake sha'awa irin gwamnatin buhari daya jagoranta a shekarar 1984-1985.

2) Bukasar tattalin arziki

Sanadiyyar faduwar farashin man fetur a shekarar 2015 gwamnati tayi kokarin ranto kudade domin biyan ma'aikata a kokarin bayyana komai yana tafiya daidai. Wanda hakan ya janyo karancin tattalin arzikin kasar har zuwa kan wannan gwamnati.

A kokarin da akayi wajen bayyana komai yana tafiya daidai kafin zuwan wannan gwamnati shiya janyo wasu daga cikin mu suke fitowa domin karyata wannan labari. Buhari ya dauki matakan da suka dace wajen farfado da tattalin arzikin kasar wanda a matsayin mu na yan kasa ya kamata mu goya masa baya. Wanda ya bayyana abubuwan da zasu farfado da tattalin arzikin ta hanyar hauhawar farashin man fetur da 700,000 a kowace tanka a rana. Wanda ya tabbata yan Nigeria bazasu daina cewa "Buhari ya lalata tattalin arzikin mu"

3) Nisan shekaru da lafiya ba shamaki bane

Abu na farko da zamuyi duba akai dangane da lafiya da shekaru shine zai iya kasancewa wa katsalandan da kuma shiga gonar daba taka ba hurumi ne na Ubangiji hatta da likitoci suna kuskure a abubuwa da dama wanda komai a hannun Allah yake. Shugabanin da suka rasu sunakan mukami (Abacha da Yar'adua) a takaice Abacha bai nuna gazawa a bangaren lafiyar sa ba kafin ya rasu.

A Zimbabwe Morgan Tsvangirai yayi amfani da lafiyar sa da shekaru wajen kamfen sa da shugaba Mugabe yana me kiransa daya yi ritaya yaje ya huta bayan makwanni da wannan magana shi Morgan din ya rasu yanada shekaru 65 yabar mugabe a raye yanada shekaru 94. Babu wani mutum da zaice wannan kamfe ne. Ba wani mutum dazai shiga gonar Ubangiji.

4) Ba'a yin watsi da jirgi a tsakiyar teku

Kirana ga dukkan magoya bayan shuganban da suka yishi a 2015 da karsuyi watsi da lamuransa. Bawai tsere ne na mita 100 zuwa sama ba tsere ne domin ceto kasar mu. Yayin da muka shiga 2019 zamu fahimci cewa mun kusa kawo karshen abun.

5. Kafa hujoji

A wajen mu wannan ba Abu bane na kayi ko ka mutu. Zamu bayyana wa yan Nigeria su ganni su kuma yanke hukunci.

Yan Nigeria sunsan daga inda matsalolin mu suke Sun san cewa ba shugaba buhari bane. Sunsan daga inda matsalar take. Ina Kira da mu hara kanmu a wannan tafiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel