Sau biyu mijina na zubar min da ciki saboda duka - Wata matar aure

Sau biyu mijina na zubar min da ciki saboda duka - Wata matar aure

Wata malamar makaranta, Romoke Ademoyegun, dake zaune a garin Ibadan din jihar Oyo ta bukaci kotu ta warware auren ta da mijinta saboda yawan jibgar ta da yake yi.

Matar ta shigar da karar mijinta, Sunday Ademoyegun, gaban kotu tana mai bukatar kotun ta raba auren su na shekaru 11 tare da bayyana cewar ta gaji da azabar da take sha a hannun mijin nata.

Ta shaidawa kotun cewar mijinta na da saurin hannu, yana yawan dukan ta bisa kowanne karamin laifi.

Sau biyu mijina na zubar min da ciki saboda duka - Wata matar aure

Sau biyu mijina na zubar min da ciki saboda duka - Wata matar aure

Ta kara da cewa, sau biyu tana barin ciki saboda dukan da mijin ke yi mata a lokutan dA take da juna biyu.

A cewar ta har guduwa tayi zuwa gidan iyayen ta amma duk da haka ya kan bi ta har can ya lakada mata duka kuma duk kokarin tsawatar masa ya ci tura.

DUBA WANNAN: Hukumar 'yan sanda ta gargadi mawakan gayu, ta basu shawarar

Duk da bai karyata ko yin musun laifin da ake tuhumar sa da aikatawa ba, Sunday, ya ce ba zai saki matar ta sa ba.

Alkalin Kotun, Henry Agbaje, ya daga sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Afrilu domin yanke hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel