Mataimakin shugaban kasa ya maye gurbin Buhari a taron majalisar ministocin Najeiya

Mataimakin shugaban kasa ya maye gurbin Buhari a taron majalisar ministocin Najeiya

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya shugabanci zaman majalisar zartarwa ta ranar Laraba, 18 ga watan Afrilu, kamar yadda Legit.ng ta kalato.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Osinbanjo ke jagorantar zaman tattaunawa a tsakanin ministocin Najeriya da sauran manyan jami’an bangaren zartarwa, tun bayan tafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari birnin Landan don halartar taron kasashen rainon Ingila.

KU KARANTA: Wani matashi ya yi ma Budurwarsa wanka da ruwan guba kan zarginta da neman maza

Sai dai ko da yake Osinbajo ya jagoranci zaman, amma ba shi da hurumin darewa kujerar da aka ware ta don zaman shugaban kasa Muhammadu Buhari, sai dai an hange shi yana zaune a kujerar dake gefen ta Buhari, kujerar da ya saba zama.

Mataimakin shugaban kasa ya maye gurbin Buhari a taron majalisar ministocin Najeiya
Osinbajo tare da Sakataren Gwmanati

An hangi Osinbajo tare da shugaban ma'aikatan gwamnati, Winfred Oyo Nta da kuma Sakataren gwamnatin tarayya, Malam Boss Gida Mustapha.

Mataimakin shugaban kasa ya maye gurbin Buhari a taron majalisar ministocin Najeiya
Taron

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu a masaukinsa dake birnin Landan, can a kasar Ingila, inda ya tafi hutu tare da halartar taron kasashen rainon Ingila.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng