Amurka ta bayyana tsoronta ga makomar Najeriya saboda karuwar zafin ra'ayi da ta'addanci a kasar

Amurka ta bayyana tsoronta ga makomar Najeriya saboda karuwar zafin ra'ayi da ta'addanci a kasar

- Hare-Haren makiyaya da na kabilanci shima ta'addanci ne

- Babban sojin Amurka mai kula da sashen Afirka ya iso Abuja

- Ya nuna damuwarsa kan yaduwar kananan makamai

Amurka ta bayyana tsoronta ga makomar Najeriya saboda karuwar zafin ra'ayi da ta'addanci a kasar
Amurka ta bayyana tsoronta ga makomar Najeriya saboda karuwar zafin ra'ayi da ta'addanci a kasar

Babban Janar din sojin Amurka da ke kula da sashen Afirka, Janar Brig.-Gen. Eugene LeBoeuf, ya nuna damuwarsa kan yadda ake sake samun zaffin ra'ayi, hare-haren ta'addanci, dama na kabilanci a fadin Najeriya da ma yankunan Afirka ta yamma.

Ya koka kan yaduwar kananan makamai, ta'adda, makiyaya/manoma, da ma hare-haren Boko Haram inda yakin yaki ci yaki cinye wa.

Wannan na zuwa ne bayan da shugaba Buhari ya ce Gaddafi ne ummul-aba-isin yaduwar makamai a nahiyar.

DUBA WANNAN: Batutuwa da shugaba Buhari ya tauna a Ingila

A baya dai, Amurka tace zata agaza wa Najeriyar wajen yaki da Boko Haram, sai dai ba'a qeyar soji ko daya daga turawan ba.

Manyan wadanda suka halarci zaman dai, sun hada da Janar Buratai, Janar Olanisakin da ma wasu manya a kasar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: