Zauren addini: Cikakken tarihin Bajimin Malamin Musulunci Imam Bukhari
Mun leka zauren addinin Musulunci inda mu ka kawo maku tarihin babban Malamin addinin nan na Hadisan Manzon Allah da ba a taba yin kamar sa ba a tarihi watau Imam Muhammad Al-Bukhari wanda ya tara Hadisan Manzon Allah sama da 600, 000.
An haifi Abu Abdullah Mohamed bin Ismail ne a Kasar Uzbekistan ta yanzu a wani Kauye mai suna Bukhara a shekara ta 194 bayan Hijira. Mahaifiyar sa ce ta rike shi lokacin da yake karami har ta kai ta kuma sa shi Makaranta inda aka ga kwazon sa ainun.
Bayan ya tashi Maraya, ya kuma yi fama da makanta na ‘dan lokaci. Yana saurayi ya haddace Kur’ani sai ya tafi Kasa mai tsarki yayi aikin Hajji tare da Mahaifiyar sa. A nan ya zauna na shekaru yana karatu kan hadisan Manzo a Garin Makkah daga nan ya bar Kasar.
KU KARANTA: Za ayi wa wani mutum bulala saboda laifin kazafi
Imam Abu Abdullah ya leka Kasar Bagadaza da Kufa da Damashk da irin su nan Masar duk wajen neman ilmi bayan ya tasa. Mohamed bin Ismail mutum ne mai kaifin hadda da kuma son karatu da riko da addini inda har ta kai sai yayi wanka in zai fadi Hadisin Annabi.
Imam Bukhari ne Mawallafin littafin nan na Sahih Al-Bukhari mai kunshe da Hadisai har 7, 275. Sahih Bukhari ne littafin da ya fi kowane littafi inganci Duniya bayan Al-Kur’ani. Bukhari ya tace Hadisan da ya tara sama da 600, 000 ya dauki 7, 000 tak ya sa a littafin na sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng