Kotu ta raban auren shekaru 10 saboda tsananin masifar wata mata

Kotu ta raban auren shekaru 10 saboda tsananin masifar wata mata

Wata babban kotu da ke zaune a unguwa Kubuwa a Abuja ta raba aure tsaknin wani Ekplador Koinya da Onajero Gloria bayan sun share shekaru goma tare saboda tsananin masifar matar.

Alkalin kotun, Bello Kawu ya kuma umurci Gloria ta mayar wa tsohon mijinta babban Janarator kirar Mikano mai samar da 12KVA da kuma fasfo na fita kasashen waje na diyar ta da ta dauke.

Kotu ta raban auren shekaru 10 saboda tsananin masifar wata mata
Kotu ta raban auren shekaru 10 saboda tsananin masifar wata mata

DUBA WANNAN: An gurfanar da wani a kotu saboda cin zarafin wani dan Majalisa a kafar Facebook

Alkalin kuma ya bukaci tsaffin ma'auratan su dena zuwa wuraren aikin juna don gudun tayar da fitina. An dai daura auren na su ne a ranar 1 ga watan Fabrairun 2008 a jihar Legas kuma suna da yara guda biyu.

Koinya ne ya shigar da karar inda ya bukaci kotu ta raba auren na sa da Gloria saboda masifar ta. Ya kara da cewa duk lokacin da wani kankanin abu ya faru, Gloria ta kan rufe shi da fada ne kuma ta kaurace masa a wajen kwanciya.

Ya roki kotu ta bashi damar rike yaran su guda biyu, kuma Gloria ta dena amfani da sunansa kuma ta dena zuwa gidansa.

A jawabinta, Gloria ta amince da rabar auren inda tace halayen Koinya sun canja kuma hakan yasa baza ta iya cigaba da zama dashi ba kamar yadda kamfanin dillanci labarai (NAN) ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel