'Yan sanda sun kashe mutum biyu a wajen wani biki

'Yan sanda sun kashe mutum biyu a wajen wani biki

Mutanen garin Anara, da ke karamar hukumar Isiala Mbano na jihar Imo sun gamu da tashin hankali a ranar Lahadi bayan wasu jami'an yan Sanda guda biyu sun harbe mutane biyu a wajen wani bikin daurin aure na gargajiya.

Harbin ke da wuya sai duk mutane suka ranta a na kare saboda su tsira da rayyukansu, Yan sandan da har yanzu ba'a gano sunayensu ba sun iso wajen daurin auren ne tare da wasu manyan mutane guda biyu kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

'Yan sanda sun kashe mutum biyu a wajen wani biki

'Yan sanda sun kashe mutum biyu a wajen wani biki

DUBA WANNAN: Za'a yiwa wani mutum bulala 80 saboda kirar surukarsa karuwa

Yan sandan sun fara harba harsashi sama ne saboda su birge manyan mutanen da sukayi wa rakiya wajen daurin auren yayinda suke lika kudi ga masu rawa a wajen daurin auren.

Rahotanni sun nuna cewa Yan sandan biyu sun rako manyan mutanen ne ba tare da izinin kwamishinan Yan sanda na jihar ba, kuma saura kiris matasan unguwar su kashe su amma iyalan amaryar suke cece su daga hannun matasan.

Wadanda suka rasu sakamakon harbin sune Ikechukwu Onwudiwe mazaunin garin Umunchi da kuma Uzochukwu Ogbuhuruzo mazaunin Ezumuoha duk a karamar hukumar Isiala Mbana a jihar Imo.

Kakakin hukumar Yan sanda na jihar, Andrew Enwerem yace kwamishinan Yan sanda, Chris Ezike, ya bayar da umurnin gudanar da bincike akan lamarin. Enwerem ya kara da cewa yan sandan sun taho ne daga jihar Ekiti kuma sun gudu bayan rigima ta kaure wajen daurin auren.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel