Da dumin sa: Muhimman abubuwa 6 da ya kamata duk dan bautar kasa ajin 'A' ya sani
Kamar yadda aka sani, tsarin bautar kasa a Najeriya dadadde ne kuma ya wajaba ga dukkan dan kasar da ya kammala karatun sa na digiri ko babbar difuloma kafin ya fara neman aiki.
A tsarin, akan yi zama na akalla sati 3 a sansanin yan bautar kasa na wata jihar da ba ta mutum ba kafin daga bisani a kai shi inda zai yi aiki har na tsawon shekara daya.
KU KARANTA: Fadar shugaban kasa tayi magana game da 'yan matan Chibok
A wannan karon ma, hukumar dake kula da yan bautar kasar ta fitar da wasu muhimman batutuwa da ya kamata dukkan 'yan bautar kasar su sani game da yin rijista a sansanin na su musamman ma dai 'yan ajin 'A'.
1. Shaidar digiri ko kuma babbar difuloma ga dukkan wanda ya kammala hakan.
2. Shaidar tantancewa na makarantar da aka gama watau Identity Card.
3. Dukkanin sahihan takardu na daliban da suka yi karatun su a waje.
4. Fasfo na tafiya kasar waje ga wadanda suka kammala karatun su a waje.
5. Dole ne dukkan takardun da aka rubuta da wani yare ba turanci ba a fassara su.
6. Shaidar lasisi daga hukumar da ta dace ga dukkan wadanda suka kammala kwasa-kwasai na musamman kamar na fannin lafiya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng