Masu garkuwa da mutane sun hallaka Dansanda tare da saci wani mutumi dan kasar Jamus a jihar Kano

Masu garkuwa da mutane sun hallaka Dansanda tare da saci wani mutumi dan kasar Jamus a jihar Kano

Wasu gungun yan bindiga sun bude ma wasu motocin ma’aikatan shahararren kamfanin gine ginen nan mallakar iyalan Dantata, watau Dantata and Sawoe, a jihar Kano, ini rahoton BBC Hausa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne da safiyar ranar Litinin 16 ga watan Afrilu akan sabon titi na jihar Kano, hanyar zuwa karamar hukumar Madobi, a lokacin da ma’aikatan kamfanin ke kan hanyarsu ta zuwa aiki a cikin jerin wasu motoci.

KU KARANTA:Baki shi ke yanka wuya: Wani matashi ya sha bulalar kazafi 80 sakamakon aibanta sirikarsa da sunan ‘Karuwa’

A wannan lokaci ne Yan bindigan suka biyo ayarin motocin, inda suka bude ma motocin wuta, a sanadiyyar haka suka hallaka wani jami’in Dansanda dake baiwa ma’aikatan tsaro.

Sai dai bayan kashe wannan Dansanda, yan bindigar sun sace wani kwararren masanin harkar gine gine, dan kasar Jamus dake cikin tawagar ma’aikatan, Michael Krangzer, tare da yin garkuwa da shi.

Shi ma Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Magaji Musa ya tabbatar da wannan hari, sa’annan ya kara da cewa tuni kwamishinan Yansandan jihar ya aika da karin jami’an Yansanda don bin sawun yan bindigar tare da ganin sun ceto mutumin da aka sace.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel