Jaruman Indiya 5 da suka karbi addinin Musulunci
Kamar yadda tarihi ya nuna mafi akasarin mutanen kasar Indiya masu bautan kumaka ne, sai daia akan dan samu sirkin musulmai a cikinsu.
Kasar Indiya na da tsohon tarihi wajen shirya fina-finai ta yadda sukayi fice a duniya baki daya. Hakan yasa muka laluba maku wasu daga cikin jaruman da suka karbi addinin Musulunci daga baya.
Ga su kamar haka:
1. Mamta Kulkarni
Ta taka gagarumar rawar gani a fina-finan Bollywood. Mijinta Vicky Goswami ya fara musulunta, da zata aure shi, sai ita ma musulunta.
2. Hema Malini
Shahararriyar jaruma ce a fina-finan Bollywood. Matar Dharmendra, mahaifiyar jaruma Esha Deol.
Hema sun yi aure da Dharmendra a 1980, amma kafin su yi aure sai da ta musulunta saboda mijin nata ma ya musulunta.
To amma Hema, har yanzu ta na bin addinin Hindu ne. Hema ta fito a fina-finai kamar Dream Girl da kuma Seeta Aur Geeta.
3. Sharmila Tagore
Sharmila Tagore, ta musulunta ne sakamakon auran mijinta Mansoor Ali Khan a shekarar 1969.
Ta sauya sunanta daga Sharmila Tagore zuwa Ayesha Sultana bayan musuluntarta.
KU KARANTA KUMA: 2019: Atiku ya kai ziyara kasar Ingila don ya karo suna
4. Monica
Fitacciyar jaruma ce a fina-finan kudancin India. Ta sanar da Musuluntarta ne a 2014, amma tun a 2010 ta karbi Musulunci. Ta sauya sunanta zuwa MG Rehima.
Mahaifinta Hindu ne, mahaifiyarta kuma kirista ce.
5. Amrita Singh
Amrita Singh ta taka gagarumar rawar gani a fina-finan Indiya. Tsohuwar matar Saif Ali Khan ce inda suka haifi 'ya'ya biyu, wato Sara Ali Khan da Ibrahim Ali Khan.
Ta taso a matsayin mai bin addinin Sikh daga bisani ta Musulunta.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng