Buhari ya kammala aikin jirgin kasa na babban birnin tarayya Abuja, zai fara aiki (Hotuna)

Buhari ya kammala aikin jirgin kasa na babban birnin tarayya Abuja, zai fara aiki (Hotuna)

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kammala aikin gina layin dogo mai tsawon kilomita 45 da siyo jirgin kasa na zamani da zai dinga kai kawo a babban birnin tarayya Abuja.

Hukumar kula da sufuri ta babban birnin tarayya Abuja ce ta bada wannan tabbaci, inda tace an kammala aiki, kuma nan bada jimawa ba jirgin zai fara jigilar mutane, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige wani Dansanda a jihar Benuwe, Yansanda 11 sun yi ɓatar dabo

Buhari ya kammala aikin jirgin kasa na babban birnin tarayya Abuja, zai fara aiki (Hotuna)

Hotuna

Sakataren hukumar, Kayode Opeifa ne ya bayyana haka a ranar Lahadi 15 ga watan Afrilu, ida yace aikin jirgin kasar dake yankin Gbazango ya kammala, kuma zai fara aiki a nan kusa, sai dai yace an dan samu tsaiko a wajen filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe.

“Mun kammala aikin tashoshin jirgin guda 12, ofisoshin ma’aikata guda 21, gadoji guda 13, lambatu guda 50, da kuma hanyoyin masu tafiyan kasa guda 9.” Inji Kayode.

Buhari ya kammala aikin jirgin kasa na babban birnin tarayya Abuja, zai fara aiki (Hotuna)

Hotuna

An tsimayin fara aikin wannan jirgin kasa na zamani, musamman ganin shi ne irin san a farko a Najeriya, kuma ya ratsa ta sabbin unguwanin Abuja dake gefen gari guda 12.

Buhari ya kammala aikin jirgin kasa na babban birnin tarayya Abuja, zai fara aiki (Hotuna)

Hotuna

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel