Wani rikakken Farfesa ya fito takarar Sanatan Yankin Daura

Wani rikakken Farfesa ya fito takarar Sanatan Yankin Daura

Idan ba ku manta ba kwanakin baya ne Sanata Mustafa Bukar wanda shi ne ke wakiltar Yankin Katsina ta Arewa a Majalisar Dattawa ya rasu. Yanzu dai mutanen da ke neman takarar Sanatan Katsina ta Arewar su na ta bayyana.

Yanzu haka dai mun kawo maku jerin wadanda ake tunani za su iya zama Sanatan na Yankin Daura nan gaba.

Wani rikakken Farfesa ya fito takarar Sanatan Yankin Daura

Tsohon 'Dan Majalisa Masanin boko kuma 'Dan siyasa zai fito takarar Sanata

1. Rt. Hon. Ya’u Umar Gojo-Gojo

Ba mamaki tsohon Kakakin Majalisar dokokin Jihar Katsina Rt. Hon. Ya’u Gojo-Gojo yana neman takarar Sanatan Yankin. Gojo-Gojo ya nemi kujerar a zaben 2015 amma a karkashin Jam’iyyar PDP kafin ya koma APC kwanan nan.

KU KARANTA: An fara rububin kujerar Marigayi Sanata Isa Wakili

2. Hon. Umar Adamu Katsayal

Farfesa Umar Katsayal yana cikin wadanda za su nemi kujerar Marigayi Musatafa Bukar. Fastocin Tsohon ‘Dan Majalisar na yankin Daura/Sandamu/Maiadua sun fara yawo. Katsayal babban malami ne a Jami’ar nan ta A.B.U da ke Zaria.

3. Hon. Nasiru Sani Zangon-Daura

Wasu kuma na ganin cewa Honarabul Zangon-Daura da ke wakiltar Baure da Zango a Majalisar Tarayya karkashin APC zai nemi kujerar. Mahaifin sa watau Alhaji Sani Zangon-Daura yana cikin manyan na kusa da Shugaba Buhari a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel