Boko Haram: Shugaba Buhari ya gaza inji Fasto Tunde Bakare
Wannan mako ne mu ke jin Fasto Tunde Bakare na cocin Later Rain Assembly da ke Garin Legas yana cewa Gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza wajen kare ran Jama’a wanda har yanzu wasu mata ke tsare hannun 'Yan Boko Haram.
Tunde Bakare a lokacin da yake magana wajen wata lacca da aka shirya a bana game da ‘Yan matan Chibok da aka sace tun 2014 ya bayyana cewa Gwamnatin Buhari da ta Jonathan ba su yi kokarin kirki wajen hana ‘Yan Boko Haram barna ba.
‘Yan Boko Haram sun kware da satar yaran makaranta musamman a Yankin Arewa maso gabas. A lokacin Jonathan an saci yara sama da 200 daga Makarantar Chibok. A Gwamnatin Buhari kuwa an saci wasu yara kwanaki a Garin Dapchi.
KU KARANTA: APC ta fito da kwamitin da za ta shirya zaben Shugabanni
Bakare yace kwanakin baya can aka yi bikin ‘Diyar Buhari da ‘Diyar Osinbajo da na wani Gwamnan Kasar ko da dai bai kira suna ba. Faston yace da ‘Ya ‘yan manyan aka sace da tuni an gano su don haka yace Gwamnatin ta gaza kare al’umma.
A karshe dai Bakare ya soki wasu kalamai na Buhari inda yace nan gaba mace za tayi mulki. Tunde Bakare yayi niyyar zama Mataimakin Shugaban kasa tare da Muhammadu Buhari a 2011 a karkashin Jam’iyyar CPC sai dai Jam’iyyar ba tayi nasara ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng